Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-29 17:01:31    
Lardin Jilin yana kokarin farfado da masana'antu

cri

Mr. Bai Yu ya kara da cewa, sabo da kamfanin farko na kera motoci na kasar Sin da ke birnin Changchun ya soma yin nazarin yin amfani da sabon makamashi a cikin motocinsu da wuri, yanzu ya riga ya samu wasu fasahohin da kamfanin yake da ikon mallakar fasaharsu. A waje daya, yana da dimbin kwararrun da suka mallaki wadannan fasahohin zamani. Sakamakon haka, kamfanin farko na kera motoci na kasar Sin da ke birnin Changchun yana nazarin fasahohin yin amfani da man fetur da sabon makamashi a cikin wata mota tare. Mr. Bai ya ce, "Mun riga mun yi nazari kan yadda za a iya yin amfani da sabon makamashi a cikin mota, musamman fasahar yin amfani da makamashi iri biyu a cikin mota daya. A cikin kayayyakin da za mu samar a shekara mai zuwa za a gano irin wannan sabuwar fasaha."

Ba ma kawai lardin Jilin na daya daga cikin tsoffin sansanonin masana'antu na kasar Sin ba, har ila yau lardi ne mai girma da ke bunkasa aikin gona a kasar Sin. Sabo da haka, lokacin da ake sabunta tsarin masana'antu a lardin, ana kuma kara saurin raya aikin gona irin na zamani. Kamfanin Hao Yue na samar da naman shanu da musulmai suke bukata na birnin Changchun wani babban kamfani ne da ke samar da naman shanu da na akuya ga duk duniya. Mr. Tian Xingqi, mataimakin babban direktan kamfanin Hao Yue ya bayyana cewa, "Sana'ar sarrafa naman shanu tana da nasaba da moriyar manoma. Yanzu, iyalai manoma dubu dari 1, wato kimanin manoma fiye da dubu dari 5 suna kiwon shanu domin samar wa kamfaninmu shanu. Yawan karin kudin da suke iya samu a kowace shekara ta hanyar kiwon shanu ya kai fiye da kudin Sin yuan miliyan 500. Bugu da kari kuma, sana'o'in samar da kunsassun kayayyaki da sufuri da gine-gine da yawon shakatawa sun kuma samu ci gaba bisa taimakawar kamfanin Hao Yue."

Mr. Tian Xingqi ya gaya wa wakilinmu cewa, kamfanin Hao Yue yana mai da hankali sosai kan ingancin naman shanu. Yana sarrafa naman shanu ne bisa ma'aunin da kasashe masu bin addinin Musulunci suke bi. Sakamakon haka, kamfanin Hao Yue yana fitar da naman shanu zuwa kasashe da yankuna fiye da 20. Mr. Tian Xingqi ya ce, "Yanzu, kamfanin Hao Yue yana fitar da naman shanu zuwa kasashe da yankuna 23. A cikin jerin shekaru 6 da suka gabata, yawan naman shanu da kamfanin ya fitar zuwa kasashen waje ya kai fiye da rabin naman shanu da duk kasar Sin take fitarwa. Sakamakon haka, kamfanin Hao Yue ya riga ya zama wani kamfani mafi girma wajen fitar da naman shanu zuwa kasashen waje a nan kasar Sin." (Sanusi Chen)


1 2 3