Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-29 17:01:31    
Lardin Jilin yana kokarin farfado da masana'antu

cri

Yau da shekaru 6 da suka gabata, kasar Sin ta soma aiwatar da shirin farfado da tsoffin sansanonin masana'antu da ke arewa maso gabashin kasar. A cikin wadannan shekaru 6 da suka gabata, ya kasance tamkar daya daga cikin sansanonin masana'antun kasar Sin, lardin Jilin ya nemi wata sabuwar hanyar farfado da masana'antu ta hanyoyin yin amfani da fasahohin zamani da samar da karin kudi ga ayyukan nazarin fasahohin zamani da kuma kyautata harkokin masana'antu.

Tsohon sansanin masana'antu na arewa maso gabashin kasar Sin da ke kunshe da lardunan Hei Longjiang da Jilin da kuma Liaoning shi ne sansanin masana'antun zamani na farko na sabuwar kasar Sin. Ya taba taka muhimmiyar rawa a fannin tattalin arziki. Amma a cikin shekarun baya, yankin arewa maso gabashin kasar Sin bai samu ci gaba kamar yadda ake fata ba a sanadiyyar dalilai iri daban daban. Bambancin da ke tsakaninsa da yankin gabashin kasar ya yi yawa. Sabo da haka, a shekara ta 2003, gwamnatin kasar Sin ta bullo da shirin farfado da yankin arewa maso gabashin kasar domin nuna goyon baya ga yankin da ya fito daga mawuyacin hali, musamman ya kara saurin daidaita tsarin sana'o'i da kuma neman sabuwar hanyar samun ci gaba.

A cikin wadannan larduna uku da ke arewa maso gabashin kasar Sin, lardin Jilin ya yi suna sabo da motoci da manyan injunan da ake kerawa a lardin. Amma tun daga shekaru 90 na karnin da ya gabata, injuna da fasahohi na koma baya sun zama matsalolin da suka addabi manyan masana'antu da kamfanoni wadanda suka taba bayar da gudummawa sosai wajen raya tattalin arzikin kasar Sin. Bayan da aka soma aiwatar da shirin farfado da masana'antun dake tsohon sansanin masana'antu na yankin arewa maso gabashin kasar Sin, wadannan masana'antu sun sake samun karfin neman ci gaba. Kamfanin kera jiragen kasa na Changchun na daya daga cikinsu. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, bisa tallafin gwamnati, wannan kamfani ya samu kudin Sin yuan biliyan 2 domin sabunta da kuma yin nazarin fasahohin zamani da yake bukata. Sakamakon haka, a cikin wasu 'yan shekarun da suka gabata kawai, wannan kamfani ya hau kan matsayin gaba da takwarorinsa a fannin nazari da kuma kera injunan jirgin kasa na zamani. Mr. Zhang Dongli, shugaban kamfanin kera jiragen kasa na Changchun ya bayyana cewa, "Muna da cibiyar nazarin sabbin fasahohi. Bisa kasancewar karfin samar da jiragen kasa da muke da shi yana kan gaba a duk duniya. Kayayyaki kirar kasar Sin da muke amfani da su ya kai kashi 76 cikin kashi dari bisa na dukkan kayayyakin da muke amfani da su a cikin kayayyakinmu. Sannan kuma galibin injunan da muke amfani da su injuna ne kirar kasar Sin."

1 2 3