Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-17 13:52:52    
Saurayi mai bakar fata da ke cikin kungiyar wasan kwallon raga ta kasar Sin

cri

Watakila kwayoyin halitta na musamman da Ding Hui yake da su sun ba wannan saurayi sharudda masu kyau da ingantuwar fasaha, amma abun da ya fi ba Zhou Jian'an mamaki shi ne shigowar Ding Hui cikin kungiyar kasar Sin ta kawo wa wannan kungiya sauye-sauye. Kafofin yada labaru sun kara mai da hankali kan wannan kungiya, ta haka karin mutane sun fara zura ido kan kungiyar kasar Sin. Ding Hui ya yi farin ciki sosai da wannan, yana mai cewar,"Na yi farin ciki da wannan. Amma ba shakka ko da ban shiga kungiyar kasar Sin ba, ya kamata ku mai da hankali kan wannan kungiya. Nan da shekaru da dama masu zuwa, kungiyar kasar Sin tana fuskantar muhimman ayyuka. Kuma kungiyarmu ta ba ni matsin lamba kadan. Shiga karon karshe na gasar wasannin Olympic da za a yi a birnin London a shekara ta 2012 shi ne aiki mafi muhimmanci gare mu."

Yanzu a sakamakon kasancewarsa, karin mutane suna zura ido kan kungiyar wasan kwallon raga ta maza ta kasar Sin. Wannan ya ba kungiyar kasar Sin babban taimako wajen tabbatar da makasudinta da samun bunkasuwa cikin dogon lokaci. Duk da haka, Ding Hui ba ya son kafofin yada labaru su mai da hankali kansa fiye da kima. Ya sha jaddada cewa, shi wani Basine ne kawai. Yana fatan za a fi mai da hankali kan fasaharsa ta yin wasa da kwallon raga da kuma ci gaban da ya samu, a maimakon siffarsa. Kamar yadda ya sha cewa, ina son in kara nuna kankan da kai.

Amma Ding Hui bai rufe zuciyarsa ga kowa ba, kuma budaddiyar zuciya ita ce ta taimaka masa wajen shiga kungiyar kasar Sin. A filin wasa, wannan saurayi ya kan yi zumudi cikin sauki, ya kan karfafa gwiwar saura. A kungiyar kasar Sin kuwa, ya kan faranta ran abokan kungiyarsa, ya kulla dangantaka mai kyau tare da su. Mambobin kungiyar kasar Sin sun lakanta masa da 'Xiaohei'. Kazalika kuma, malaman horas da wasanni na kungiyar kasar Sin su ma suna kishin wannan saurayi sosai. Zhou Jian'an ya damu da cewa, zura ido da kafofin yada labaru suke yi kan Ding Hui fiye da kima zai kawo illa ga tunaninsa. Tare da yi masa gargadi, Mr. Zhou ya nuna wa Xiaohei fatan alheri sosai, inda ya ce,"Yanzu, Ding Hui ya aza harsashi mai kyau domin zama fitaccen dan wasan kwallon raga da ya iya kare kwallo ne kawai. Amma ko zai iya zama wanda zai yi fice ko a'a, wannan ya dogara ga kokarin da zai nuna. Saboda ma ne wani saurayi ne kawai, bai taba shiga gasanni da yawa ba, kuma yana bukatar ci gaba da kyautata fasaharsa. Yana bukatar daga matsayinsa a fannoni da dama."

Ko da yake a yayin gasar wasannin Olympic da aka yi a nan Beijing a shekarar da ta gabata, a karo na farko ne kungiyar wasan kwallon raga ta maza ta kasar Sin ta shiga wannan muhimmiyar gasa, kuma ta zama ta biyar a karshe dai, amma kungiyar wasan kwallon raga ta maza ta kasar Sin ta iya samun damar shiga karon karshe na shirin wasan kwallon raga na gasar wasannin Olympic ne domin birnin Beijing na kasar Sin ya sami bakuncin shirya gasar wasannin Olympic a shekarar bara. A gaskiya yanzu kungiyar kasar Sin tana kasancewa a rukuni na biyu kawai a fannin wasan kwallon raga na maza a duk duniya. Ko a nahiyar Asiya kuma, tana fuskantar kungiyoyin kasashen Korea ta Kudu da Japan da Australia masu karfi. Shi ya sa kokarin shiga gasar wasannin Olympic bisa karfinta shi ne makasudin da kungiyar wasan kwallon raga ta maza ta kasar Sin da Ding Hui yake ciki ta tsara bisa abubuwan gaskiya. Dangane da gasar wasannin Olympic da za a yi a birnin London na kasar Birtaniya a shekara ta 2012, Ding Hui mai shekaru 20 da haihuwa ya nuna fatan alheri matuka da cewa,"Makasudinmu shi ne shiga gasar wasannin Olympic bisa karfinmu na gaskiya. Shi ne makasudinmu mafi muhimmanci a halin yanzu."(Tasallah)


1 2 3