Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-17 13:52:52    
Saurayi mai bakar fata da ke cikin kungiyar wasan kwallon raga ta kasar Sin

cri

Ko da yake baya ga Hua Tian, dan wasan fasahar hawan doki da iyayensa suka zo daga kasashen Birtaniya da Sin, da Ge Misha, dan wasan kankara na salo-salo da iyayensa suka zo daga kasashen Rasha da Sin sun shiga gasannin duniya a matsayin 'yan wasan kasar Sin, amma kasancewar Ding Hui cikin kungiyar wasan kwallon raga ta maza ta kasar Sin ya sanya wannan saurayi ya zama dan wasa barbarar yanyawa na farko a tarihin kungiyar wasan kwallon raga ta maza ta kasar Sin.

Mahaifin Ding Hui wani dan kasar Afirka ta Kudu ne, kuma mahaifiyarsa wata tsantsar Basiniya ce da take zaune a birnin Hangzhou. Ding Hui mai shekarun 20 da haihuwa ya zama wani Basine a lokacin da yake karami, kuma ya girma a birnin Hangzhou. Shi ya sa wannan saurari mai bakar fata ya iya Sinanci da kuma yaren birnin Hangzhou kwarai da gaske. A lokacin da yake karami, Ding Hui ba shi da koshin lafiya. Shi ya sa mahaifiyarsa ta sa shi cikin makarantar motsa jiki domin kyautata lafiyarsa, tun daga nan Ding Hui ya kulla dangantaka mai danko a tsakaninsa da wasan kwallon raga. Ba a taba tunanin cewa, a sakamakon jikinsa mai kyau, Ding Hui ya taba shiga kungiyoyin kasar Sin na matsayin yara da matasa ba, yanzu wani mamba ne na kungiyar kasar Sin a hukunce.

Dangane da dalilin da ya sa aka shigar da shi a cikin kungiyar kasar Sin, Zhou Jian'an, babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin ya bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne Ding Hui ya yi fice ta fuskar sarrafa jiki da fasaha. Inda ya ce,"Ding Hui ya san kwallon raga sosai. Ya aza harsashi mai kyau. Ya gwanance ne a fannonin mika kwallo da kare kwallo. Wannan wata kyauta ce da Allah ya ba shi a matsayin dan wasan kwallon raga na musamman da ya iya kare kwallo kawai, haka kuma shi ne abun da 'yan wasan kwallon raga suka fi bukata. Ban da wannan kuma, yana da kuzari, ya iya sarrafa jikinsa matuka, kuma ya iya koyon abubuwa cikin sauri."

1 2 3