Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-02 22:38:13    
Kasar Sin ta samu dimbin nasarori a fannin kare al'adun tarihi da aka gada daga kaka da kakanni da ba na kayayyaki ba

cri

Gwamnatin kasar Sin ta soma ayyukanta na kokarin kiyaye al'adun tarihi da aka gada daga kaka da kakanni da ba na kayayyaki ba ne tun shekaru kalilan da suka gabata, haka kuma tana aiwatar da matakai daban-daban domin nuna goyon-baya da baiwa masu gado kwarin-gwiwar su gudanar da ayyukan gadon al'adun tarihi da aka gada daga kaka da kakanni. Mista Zhou Heping, mataimakin ministan kula da harkokin al'adu na kasar Sin ya nuna cewa, kwalliya ta riga ta biya kudin sabulu a fannin kare al'adun tarihi da aka gada daga kaka da kakanni da ba na kayayyaki ba, inda ya ce: "Gwamnatin kasar Sin ta dade tana maida hankali sosai kan aikin kiyaye al'adun tarihi da aka gada daga kaka da kakanni da ba na kayayyaki ba. Yanzu kasar Sin ta kafa yankunan gwaje-gwaje guda hudu na kiyaye al'adun gargajiya da muhallin halittu, haka kuma tana kokari ba kakkautawa wajen tsara dokokin shari'a a wannan fanni."

1 2 3