Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-02 21:00:03    
Dukiyoyin birnin Lanzhou

cri

Rawayan Kogi ya yi kama da wata jijiya ta birnin Lanzhou, ya ba da babban tasiri ga wannan birni. Kwale-kwalen da aka yi da fatar tunkiya da wili na ban ruwa da gadar karfe irin na Rawayan Kogi da sauran abubuwan musamman da suka nuna halin musamman na al'adun Rawayan Kogi sun taba ko kuma ya zuwa yanzu suna taka muhimmiyar rawa a zaman rayuwar mazauna birnin Lanzhou.

A bangaren Rawayan Kogi da ya ratsa birnin Lanzhou, a da babu gada. Shi ya sa mazauna Lanzhou masu hikima da yin aiki tukuru suka kirkiro kwale-kwalen fatar tunkiya domin ketare Rawayan Kogi. An yi dubban shekaru ana amfani da wannan hanya domin ketare Rawayan Kogi, wanda aka mayar da shi tamkar wani zuzzurfan kwari na asali da ruwa ke taruwa. Wannan kwale-kwalen da aka hada da fatar tunkiya ya taba zama a matsayin muhimmin ababen hawa ne ga mutane a fannonin zirga-zirga da kuma sufuri a zamanin da.

Fan Wen, shugaban hukumar madaba'a ta birnin Lanzhou ya yi karin bayanin cewa, "Kwale-kwalen fatar tunkiya ya fi taka rawa a fannin yayata al'adu, in an kwatanta da rawar da ya taka a fannin sufuri. Garina na Lanzhou yana cikin bangare na sama na Rawayan Kogi, inda ake da yawan kabilu. Kirkiro kwale-kwalen da aka yi da fatar tunkiya da hada shi sun sanya kabilu daban daban na cikin yanayin cude-ni-in-cude-ka a harkokin al'adu. A karshen shekarun 1950 da kuma farkon shekarun 1960, an taba yin amfani da irin wannan kwale-kwalen fatar tunkiya domin sufurin na'urori da yawa. Abin da ya fi nuna muhimmiyar rawar irin wannan kwale-kwale shi ne a yayin da aka kafa masana'antu a kwarin Qingtongxia a jihar kabilar Hui ta Ningxia mai cin gashin kanta ta Sin, ba a iya yin jigilar na'urar da nauyinta ya kai ton ashirin zuwa talatin ba a sakamakon rashin hanyar dogo a kusa da kwarin Qingtongxia. Shi ya sa aka yi jigilar wannan na'ura a birnin Lanzhou, daga baya, an yi amfani da kwale-kwalen fatar tunkiya domin kai mata a kwarin Qingtongxia daga Lanzhou ta hanyar Rawayan Kogi."

Ingantattun al'adu da aka samu a Rawayan Kogi suna da dadadden tarihi. Baya ga kwale-kwalen fatar tunkiya da wili na ban ruwa da sauran ababen hawa da na kawo albarka da na zaman rayuwa, wadanda jama'ar Sin suka kirkiro bisa hikimarsu, mujallar Du Zhe da ta bullo yau da shekaru 20 ko fiye da suka wuce, kuma ta shahara sosai a gida da wajen kasar Sin ta fi nuna halin musamman na al'adu.

Yau da shekaru 27 da suka wuce, wani babban edita da wasu daliban da suka gama karatu a sashen nazarin kimiyya a jami'a sun kafa kamfanin buga mujallar Du Zhe, wadda aka kira ta "Du Zhe Wen Zhai", wato wata mujallar da ake buga wa masu karatu. A farkon lokacin wallafa mujallar, ana sayar da dubu 30 ne kawai. Amma a cikin ko wadanne shekaru 3 masu kamawa, yawan mujallar da ake bugawa na ta karuwa da dubu 500, wanda ya samar da matsayin bajimta a tarihin kasar Sin na buga mujalloli. Yau wato bayan shekaru 27, yawan mujallar Du Zhe da aka buga ya zama na farko a tsakanin mujalloli masu nau'o'i dubu 9 ko fiye a duk fadin kasar Sin. A halin yanzu, mujallar Du Zhe ba kawai wata shahararriyar mujalla ba ce, har ma ta iya nuna halin musamman na birnin Lanzhou ta fuskar al'adu, ta riga ta zama katin suna na wannan birni.

Ba da tabbacin ingancin mujallar Du Zhe har na tsawon shekaru 20 ko fiye ya haifar da kyakkyawan sunanta. Peng Changcheng, babban edia na yanzu na mujallar ya gaya mana cewa,"Bayan shiga cikin karni na 21, mujallarmu ta Du Zhe ta fito da wani take, wato samar wa mutanen Sin wani littafin da ya iya karfafa zukatansu. Za mu ci gaba da bude idonmu da kuma nuna sahihanci."

Mujallar Du Zhe ta yi kama da abinci ne ga mazauna Lanzhou a tunani. In an tabo magana kan abincin da mazauna Lanzhou kan ci, tabbas ne za a tuna da taliyar naman sa nan da nan. Mazauna Lanzhou suna son cin taliya, musamman ma taliyar da suka dafa tare da naman sa. Taliyar naman sa da mazauna Lanzhou suka dafa ya yada sunanta sosai. Yanzu taliyar naman sa irin ta Lanzhou ta riga ta zama wani irin cincin na musamman da ake iya gani a ko ina a kasar Sin. A birnin Lanzhou, taliyar naman sa tana gaba da sauran abinci. Mazauna Lanzhou su kan ce, ba za su iya jure wahalar rashin taliyar naman sa har na tsawon kwanaki 3 ba."A wasu lokuta, bayan na kammala aikina, na koma Lanzhou daga wani wuri, ba na komawa gida, sai na je gidan sayar da taliyar naman sa kai tsaye."

"A ko ina a kasarmu, muna iya kallon allunan gidajen sayar da taliyar naman sa, har ma a kololuwar babban tsaunin Taishan."

An yi shekaru sama da 90 ana sayar da taliyar naman sa a Lanzhou. Wanda ya kago taliyar naman sa a Lanzhou wani musulami ne mai suna Ma Baozi. Yau Hai Fuchang, wanda ya gaji fasahar dafa taliyar naman sa irin ta Lanzhou daga kakaninsa Ma Baozi ya fito da sabon ma'auni na dafa taliyar, wanda ya fi dacewa da dandanon mutanen zamanin yau. A ganinsa, taliyar naman sa ba kawai wani irin kayan abinci ne ba, ta rigaya ta zama alamar al'adun abinci.

To, masu sauraro, karshen ziyararmu a nan kasar Sin a yau ke nan. Idan a garinku, akwai wani wurin yawon shakatawa ko kuma wani irin kayan abinci da kuke sha'awa sosai, ko kuma garinku shi kansa yana da ban sha'awa sosai, to, don Allah ku aiko mana wasika kan haka, za mu karanta wasikunku a shirinmu a nan gaba domin jama'a su fahimta.


1 2