Masu sauraro, barka da war haka! Yanzu kuna sauraren shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin ne da mu kan gabatar muku a ko wace ranar Talata. Ni ce Tasallah da na kan jagorance ku domin zagayawa a nan kasar Sin.
A kan kira Rawayan Kogi tamkar kogi ne mahaifin al'ummar kasar Sin. Birnin Lanzhou da ke arewa maso yammacin kasar Sin birni ne mafi girma a bangare na sama na Rawayan Kogi, wanda kogin ya ratsa shi. A cikin shirinmu na yau, za mu je birnin Lanzhou tare domin kara samun fahimta kan dukiyoyin wannan birni guda 3.
Birnin Lanzhou na kasancewa a bangare na sama na Rawayan Kogi, kuma shi ne hedkwatar lardin Gansu. Sa'an nan kuma, wannan birni ya taba nuna muhimmanci sosai a kan hanyar safarar siliki ta kasar Sin ta zamanin da, shi ya sa wayewar kai na Rawayan Kogi da na hanyar siliki suka ba da babban tasiri a wannan birni.
Babban tsaunin Baitashan na birnin Lanzhou ne ta arewa, a kudu kuwa, akwai babban tsaunin Gaolanshan. Birnin Lanzhou mai tsayi amma maras fadi yana kasancewa a tsakanin wadannan manyan tsaunuka 2. Rawayan Kogi ya ratsa wannan birni, ya raba shi zuwa kashi 2. Kasancewar birnin Lanzhou a tsakanin manyan tsaunuka 2 yayin da wani kogi ya ratsa shi ta sanya wannan birni ya zama wuri ne mai dacewa domin gudun zafi a lokacin tsananin zafi.
Wurin musamman da birnin Lanzhou yake kasancewa da isasshen hasken rana da kuma yawan zafi mai dacewa sun taimaka wa Lanzhou ya zama birni ne mai arzikin 'ya'yan itatuwa. Birnin Lanzhou ya sami albarkar kankana nau'in Honey Dew melon a Turance da wata irin kankana ta daban da ake samu a Rawayan Kogi kawai wato Huang He Mi Gua da kuma wani dan itace na Pear da ake samu a Rawayan Kogi kawai wato Dong Guo Li da sauran 'ya'yan itatuwa masu dandano. A ko wane watan Yuli da na Agusta, birnin Lanzhou kan karbi matafiyan da suka zo daga sassa daban daban, wadanda suka ji dadin sanyi da dandana 'ya'yan itatuwa masu zaki a lokacin matukar zafi.
Baya ga wurare masu ni'ima da ke cikin birnin Lanzhou, dukiyoyi 3 da wannan birni ke da su su ma sun sami gindi zama a zukatan mutane, wato Rawayan Kogi da mujallar "Masu Karatu" wato Du Zhe ta bakin Sinawa da kuma taliyar da mazauna birnin Lanzhou kan dafa tare da naman sa wato Niu Rou Mian.
1 2
|