Abin musamman da ya kamata a ambata shi ne a karo na farko ne an bude kofar bikin cinikin kayayyakin da ake shige da fice na Guangzhou ga 'yan kasuwa na kasar Sin wadanda suke son sayen kayayyaki a gun bikin. A lokacin da ake yakar rikicin kudi na duniya, an yi amfani da wannan dandalin baje koli domin sa kaimi ga wadanda suke son sayar da kayayyaki kirar kasar Sin a kasuwar cikin gida. Sabo da haka, wannan gwaji ya samu maraba daga wadanda suka halarci bikin. Lokacin da yake ganawa da 'yan jaridu, Mr. Jiang Guoyuan, mataimakin babban direktan kamfanin hannun jari na rukunin sada zumunci na Guangzhou ya bayyana cewa, wannan bikin cinikin kayayyaki na Guangzhou ya samar da kyakkyawan dandali da dama ga 'yan kasuwa. Mr. Jiang ya ce, "Da farko dai za mu iya habaka sabbin hanyoyin shigar da kayayyaki, wato za mu iya sanin karin kyawawan kayayyaki da wasu masana'antu. Sabo da haka, za mu iya shigar da kayayyakin da bakinmu suke bukata a nan gaba. Kuma za mu iya kara ire-iren kayayyakinmu. Yanzu, masana'antun da suka fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje a da sun soma tuntubarmu domin kafa wata huldar hadin gwiwa a tsakaninmu."
Jami'in da ke kula da bikin cinikin kayayyakin da ake shige da fice na Guangzhou ya bayyana cewa, wannan tsarin sada cinikin waje da na gida da aka kafa a karo na farko ya samu sakamako sosai. A gun tarurrukan tattaunawa sau biyu da aka yi, manyan kasuwanni da manyan shaguna da kantuna masu sayar da kayayyaki na sari na cikin gida fiye da dari 2 da 'yan kasuwa na cikin gida da na Hongkong fiye da 700 sun sadu da juna a karo na farko. A gun taron tattaunawa a karo na farko kadai, yawan darajar kwangilolin da aka kulla ya kai kudin Sin yuan miliyan 460. Mr. Mu Xinhai, kakakin bikin baje koli na Guangzhou ya ce, za a ci gaba da wannan tsari a nan gaba. "Bisa fasahohin da muka samu a yayin wannan biki, za mu ci gaba da neman karin hanyoyin da suke dacewa domin raya cinikin waje da na gida tare."
Ka'idojin da kasar Sin take bi wajen yin cinikin waje da na gida suna da bambanci, sabo da haka, wani babban jami'in ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana fatan za a iya ba da hidima ga wadanda suke son sayar da kayayyakin da ake fitar da su zuwa kasashen waje a kasuwar cikin gida ta hanyoyin zamani da dukkan kasashen duniya suke sabawa. A waje daya, ya kamata masana'antun da suke fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje su kara mai da hankali kan tamburan kayayyakinsu da kuma horar da ma'aikatan da suke kwarewa kan sayar da kayayyakinsu. Sakamakon haka, za su iya mayar boyayyun bukatu da su zama damar kasuwanci a nan gaba.
An labarta cewa, tun daga bikin cinikin kayayyakin da ake shige da fice na Guangzhou mai zuwa, za a gajerce tsawon lokacin bikin, wato za a yi kwanaki 21, ba kwanaki 23 na yanzu ba wajen yin wannan bikin cinikin kayayyakin da ake shige da fice na Guangzhou. (Sanusi Chen) 1 2 3
|