Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-02 09:55:42    
Ana neman sabuwar hanyar bunkasa bikin baje koli na Guangzhou

cri

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, lokacin da kasuwannin gargajiya suke ragu, yawan kudaden cinikayya da aka yi a sabbin kasuwannin duniya ya samu karuwa. Mr. Mu Xinhai, kakakin bikin cinikin kayayyakin da ake shige da fice na Guangzhou ya bayyana cewa, "A fannin sabbin kasuwanni masu tasowa, yawan kudin cinikayya da aka yi a tsakanin kasar Sin da kasar Argentina ya kai dalar Amurka biliyan 380, wato ya karu da kashi 10 cikin kashi dari. A waje daya, irin wannan adadi a tsakanin kasar Sin da kasar Indiya ya kai dalar Amurka miliyan 770, wato ya karu da kashi 6.2 cikin kashi dari. Sannan a tsakanin kasar Sin da kasashe mambobin kungiyar Asean wannan adadi ya kai kusan dalar Amurka biliyan 2. wato ya karu fiye da kashi 7 cikin kashi dari."

A yayin wannan biki, kayayyaki masu fasahohin zamani sun fi jawo hankalin mutane. Kamfanin saka na Zexiang na lardin Shandong ya yi shekaru 6 yana nazari kuma ya samu sabuwar fasahar zamani ta yin sabon salon kayayyakin saka. Sabo da haka, a yayin bikin cinikin kayayyaki na Guangzhou da aka yi a shekarar da ake ciki, kayayyakin saka da kamfanin saka na Zexiang na lardin Shandong ya samar ya jawo hankalin 'yan kasuwa sosai. Mr. Ma Yucheng, shugaba kuma babban direktan kamfanin saka na Zexiang na Shandong ya ce, "A yayin wannan bikin cinikin kayayyakin da ake shige da fice na Guangzhou, sakamakon da muka samu ya yi kyau. Sabo da haka, muna farin ciki kwarai da gaske. Muna da fasahohin zamani, 'yan kasuwa na kasashen waje sun mai da hankali sosai kan sabbin kayayyakinmu. Sakamakon da muka samu ya fi wanda aka yi hasashe kyau."

A waje daya kuma, a sanaddiyar barkewar cutar mura mai nau'in A (H1N1) a duk duniya. Yawan naurorin aikin likita da ake bukata a kasuwa ya samu karuwa cikin sauri. Sakamakon haka, a yayin wannan biki, yawan kudaden cinikin naurorin aikin likita da kayayyakinsu na gyara da aka yi ya kai dalar Amurka miliyan 220, wato ya karu da kashi 34.7 cikin kashi dari. Daga cikinsu, yanzu an riga an sayar da kusan dukkan kayayyakin yakar cutar mura mai nau'in A (H1N1), kamar su mayanin baki da hanci da naurar binciken zafin jiki da magani mai kashe kwayoyin cuta. Yanzu babu saura a cikin dakunan ajiye kayayyaki na galibin masana'antu. Mr. Wang Songqiao, direktan kamfanin shige da fice na Henxiang da ke birnin Suzhou, ya ce, "Sabbin baki 'yan kasuwa da suke son sayen kayayyakinmu sun yi yawa. Wasu daga cikinsu ba su taba cinikin mayanin baki da hanci ba a da. Amma sabo da yanzu kusan dukkan kasashen duniya suna bukatar mayanin baki da hanci cikin gaggawa, wasu 'yan kasuwa sun zo bikin cinikin kayayyaki na Guangzhou ne domin sayen mayanin baki da hanci musamman. Yanzu galibin masana'antun yin mayanin baki da hanci sun samu kwangilolin da za su iya kammala su sai karshen watan Yuni na shekarar da ake ciki. Sakamakon haka, farashin danyun kayayyakin yin mayanin baki da hanci ya kuma karu, farashin mayanin baki da hanci ma ya samu karuwa."

1 2 3