Bisa kididdigar da aka yi, an ce, mutane fiye da dubu 69 sun mutu a sanadiyyar bala'in girgirzar kasa da aka yi a ran 12 ga watan Mayu na shekara ta 2008, tare da mutane fiye da dubu 17 da suka bace. Jimillar hasarar tattalin arziki da aka yi kai tsaye a cikin bala'in ta kai kudin Sin yuan biliyan 840. Bayan wannan bala'in girgizar kasa na Wenchuan, gwamnatin kasar Sin ta bayar da burin da dole ne za a cimma lokacin da ake sake raya yankunan, wannan buri shi ne "kowane iyali zai samu gidan kwana da guraban aikin yi da kuma ba da tabbaci ga dukkan mutane tare da inganta manyan ayyukan yau da kullum da ci gaban tattalin arziki da kuma kyautatuwar yanayi mai daukar sauti".
Bisa binciken da aka yi, an ce, ya zuwa yanzu, a lardunan Sichuan da Gansu da Shaanxi da suka gamu da bala'in, an riga an inganta kusan dukkan gidajen manoma. Kuma an riga an kammala aikin gina sabbin makarantu iri iri da yawansu ya kai kashi 75 cikin kashi dari daga cikin dukkan makarantun da za a sake ginawa.
Lokacin da yake hangen nesa, shugaba Hu Jintao ya ce, har yanzu ayyukan sake raya yankunan da suka gamu da bala'in suna da nauyi sosai. Ya kamata a kara karfi da saurin sake raya su. Mr. Hu ya ce, "Ayyukan sake raya yankunan da suka gamu da bala'in girgizar kasa suna shafar moriyar jama'a wadanda suke zaune a yankunan, kuma suna shafar nan gaba na wadannan yankuna. Sabo da haka, ya kamata a kara karfi da sauri da kuma warware matsalolin da ke kasancewa a gabanmu domin kokarin yin amfani da shekaru 2, amma ba shekaru 3 da muka furta a da ba wajen kammala dukkan ayyukan sake raya yankuna." (Sanusi Chen) 1 2
|