Yau, wato ran 12 ga watan Mayu, rana ce ta cika shekara 1 da aka yi girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. Sabo da haka, a wannan rana, gwamnatin kasar Sin ta shirya bikin tunawa a garin Yingxiu na gundumar Wenchuan da ke lardin Sichuan. A gun bikin, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya bayar da jawabi, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi kokarin kammala ayyukan sake raya yankunan da suka gamu da bala'in girgizar kasa a cikin shekaru 2, ba a cikin shekaru 3 bisa tsohon shirin da aka tsara ba. yanzu ga wani cikakken bayani game da bikin.
Kimanin karfe 2 da minti 20 na yau da rana, mai busa karamin kakaki ya soma busa "kidan begen iyali" a gaban buraguzan gine-gine na makarantar midil ta Xuankou da ke garin Yingxiu. Yau da shekara 1 da ta gabata, garin Yingxiu ya zama sai buraguzai a sanadiyyar afkuwar bala'in girgizar kasa. A cikin dukkan mutane dubu 10 na garin, mutane dubu 3 kawai ne suka tsira daga bala'in. Yau a cikin kidan nuna tausayi, shugaba Hu Jintao da mataimakin firayin minista Li Keqiang da sauran shugabannin kasar Sin sun je garin Yingxiu don tunawa da mutanen da suka mutu a sanadiyyar bala'in girgizar kasa.
A gun bikin, Mr. Hu Jintao ya yi wani jawabi, inda ya bayyana cewa, a cikin shekara 1 da ta gabata, gwamnati da jama'ar kasar Sin da 'yan uwa Sinawa da suke zaune a gida da kuma a ketare dukkansu sun hada kan juna wajen fama da bala'in da yin ayyukan sake raya yankunan da suka gamu da bala'in. Gamayyar kasa da kasa sun kuma nuna goyon baya da kuma ba da tallafi sosai. Mr. Hu ya ce, "Mun tsara shirin sake raya yankunan da suka gamu da bala'in bisa ka'idojin sanya mutane a gaban kome da girmama ka'idojin halittu da tsara shiri bisa manyan tsare-tsare da kuma ilmin kimiyya. Kuma nan da nan mun tsara manufofi da matakai a jere domin tallafawa yankunan da suka gamu da bala'in. Ya zuwa yanzu, an riga an samu muhimmin kwarya-kwaryan sakamako wajen ayyukan sake raya yankunan. Jama'ar da suka gamu da bala'in sun sake samun zaman rayuwa mai kyau."
1 2
|