
An ce, yanzu hukumar nazarin magunguna ta Shanghai a karkashin cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Sin da jami'ar koyon ilmin magungunan gargajiyar Sin da ke birnin Tianjin da kuma kamfanin harhada magunguna ta Tongrentang da dai sauran sassa da dama suna daukar nauyin aiwatar da wannan shiri. Mr.Zhang Boli, shugaban jami'ar koyon ilmin magungunan gargajiyar Sin da ke birnin Tianjin, ya ce,"magungunan gargajiyar Sin suna daukar halin musamman na kasar Sin, kuma sun kasance ainihin kyawawan al'adunmu, haka kuma wani fannin da ke da karfin takara a duniya. Za mu mai da hankali a kan kirkiro sabbin magungunan gargajiya, musamman ma ta fannin magungunan hanyoyin jini na zukata da na kwakwalwa, kuma yawan kudin da aka zuba ya kai kimanin kudin Sin yuan miliyan 10.(Lubabatu) 1 2 3
|