
Mr.Sang Guowei, wanda ke kula da wannan shiri ya ce, masu ilmin kimiyya na kasar Sin za su yi nazari a kan manyan cututtuka 10 da ke lahanta lafiyar jama'a, kan wani kokari na kirkiro sabbin magunguna masu inganci kuma saukin farashi. Kamar yadda ya fada,"Za mu yi nazari a kan manyan cututtukan da ke lahanta lafiyar jama'a, kan yunkurin kirkiro wasu magunguna 30 da muke mallakar ilmin kirkiro su, don cimma babban cigaba ta fannin kirkiro sabbin magunguna. Na biyu, za mu kafa wani dandali na yin nazari kan magunguna tsakanin kasa da kasa, don inganta karfin kasarmu ta fannin kirkiro da magunguna. Har wa yau kuma, za mu raya wasu masana'antun harhada magunguna da ke da karfin takara da takwarorinsu na kasashen duniya."
Yanzu kasar Sin na da dubban masana'antun harhada magunguna, amma akasarinsu ba su da sassan nazari, sabo da haka, sun kasance marasa karfi wajen kirkire-kirkire. A cikin irin wannan hali ne, yanzu kashi 97% na magungunan da aka harhada a Sin sun kasance masu kwaikwayo na magungunan kasashen waje, wadanda kuma ke da daraja. Mr.Wan Gang, ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin ya ce, babban shirin kirkiro sabbin magunguna da ake aiwatarwa zai iya sauya irin halin da ake ciki, ya ce,"sabbin magungunanmu da yawa irinsu na kari da zuciya da kuma maganin kashe kwayoyin cuta, muna dogara ga shigowa da su daga kasashen waje, ga shi kuma suna da daraja, wadanda ke dora nauyi sosai a kan kasarmu da kuma jama'armu. Don daidaita matsalolin, ya zama dole mu kara karfinmu wajen kirkire-kirkiren magunguna, ta yadda masana'antun harhada magunguna namu za su iya samar da magungunan da muke kirkiro. Wannan ya kasance wani muhimmin mataki na tabbatar da lafiyar jama'a, haka kuma mataki ne da muka dauka wajen tinkarar matsalar kudi da kuma gaggauta tsarin gyaran masana'antun harhada magunguna."
1 2 3
|