Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-22 16:34:17    
Gamayyar kasa da kasa na sa lura kan aikin hadin gwiwar sojojin tekun kasashe daban daban da ake yi a kasar Sin

cri

Kasar Faransa ita ma ta tura jirgin ruwan yaki don halartar aikin hadin kai da ake yi a birnin Qingdao. Kamar dai yadda kamfanin dillancin labaru na Faransa na AFP ya yi sharhi da cewa, kasar Sin za ta nuna jirgin ruwan yaki da ke tafiya a karkashin ruwa mai yin amfani da makamashin nukiliya a karon farko, amma ba don kambama kanta ba. Sa'an nan an ambaci alkawarin da kasar Sin ta yi na raya karfin soja don zaman lafiya, kuma za a aiwatar da aikin karkashin sa ido da sauran kasashe suke mata, don kada wata kasa ta dauki abin tamkar barazana.

A baya ga haka kuma, kasar Rasha, bisa matsayinta na makwabciyar kasar Sin, ta tura jiragen ruwan yaki zuwa wurin da ake aiwatar da aikin hadin kai. Sa'an nan kafofin watsa labaru na kasar Pakistan sun ba da labarin cewa, kasar Pakistan ta dora muhimmanci sosai kan aikin. Baya ga tura jiragen ruwan yaki 2 halartar aikin, Noman Bashir, hafsan hafsoshin sojojin tekun kasar shi ma ya kawo ziyara kasar Sin. Sa'an nan bangaren Pakistan ya nuna yabo kan karfin da sojojin tekun kasar Sin suke da shi.

1 2 3