Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-21 22:20:35    
Yadda 'yan kabilar Lisu ta kasar Sin ke bukukuwan taya murnar sallar bazara

cri

Tare da karatowar sallar bazara, 'yan kabilar Lisu su kan rera wakokin gargajiya domin bayyana fatan alheri ga kowa da kowa a sabuwar shekara.

Domin taya murnar sallar bazara ta kowace shekara, 'yan kabilar Lisu su kan shirya wani biki na gargajiya mai suna bikin "Zaotang", ko kuma bikin "Chunyu". A ranar 2 ga watan farko na sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, 'yan kabilar Lisu suna yin gangami a kewaye da tafkin ruwan dumi, suna yin wanka, suna rera waka, domin kawar da gajiya da maraba da sabuwar shekara. Mista Hu Acai ya bayyana cewa, bikin "Zaotang" wanda ya fi shahara tsakanin 'yan kabilar Lisu shi ne, bikin da aka yi a tafkin ruwan dumi na Denggeng dake gundumar Lushui ta yankin Nujiang mai zaman kansa na lardin Yunnan, inda ya ce: "A kan shirya gagarumin bikin 'Zaotang' a tafkin ruwan dumi na Denggeng, don haka bikin ya yi suna sosai. Yayin da ake shirya bikin, halin annashuwa ya game a ko'ina."

Samari 'yan kabilar Lisu sun fi sha'awar bikin "Zaotang" ko bikin "Chunyu". Saboda a gun bikin, samari suna iya yin gasar rera waka, da neman masoyansu. Chu Runqin, wata 'yar kabilar Lisu tana sha'awar bikin "Zaotang" kwarai da gaske, inda ta ce: "A gun bikin 'Zaotang' da ake yi a tafkin ruwan dumi na Denggeng, 'yan uwa na kabilar Lisu suna taruwa, da shirya wasanni iri-iri, ciki har da harba kibau, da wasan taka-juye. Maza da mata, tsoffi da kanana, dukkanmu muna so mu je wurin, ta yadda za mu yaukaka zumuncinmu."

1 2 3