Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-21 22:20:35    
Yadda 'yan kabilar Lisu ta kasar Sin ke bukukuwan taya murnar sallar bazara

cri

A cikin shirinmu na makon da ya gabata, mun dai gabatar muku da wani bayani na musamman dangane da yadda 'yan kabilar E'lunchun suke nasu bukukuwan taya murnar sallar bazara. A cikin shirinmu na yau, ina so in kawo muku wani bayani na daban game da yadda kabilar Lisu ta kasar Sin ke bukukuwan taya murnar sallar bazara.

Kabilar Lisu, wata karamar kabila ce wadda ta tsallake bakin iyakokin kasar Sin da wasu kasashen kudu maso gabashin nahiyar Asiya, ciki har da kasashen Burma, da Thailand, gami da Laos. 'Yan kabilar Lisu wadanda suke zaune cikin yankin kasar Sin suna zaune ne a lardunan Yunnan da Sichuan, suna da nasu yare da rubutattun kalmomi. 'Yan kabilar Lisu suna da wani biki na gargajiya mai suna bikin Baishi domin taya murnar shigowar sabuwar shekara, amma sakamakon cudanya da mu'amalar da ake yi tsakanin 'yan kabilar Lisu da sauran mutanen kananan kabilu, sannu a hankali 'yan kabilar suka soma maida hankulansu kan bikin gargajiya na al'ummar kasar Sin wato sallar bazara.

Yankin Nujiang mai cin gashin kansa na kabilar Lisu yana arewa maso yammacin lardin Yunnan na kasar Sin, inda 'yan kabilar Lisu kimanin dubu 500 suke zaune. 'Yan kabilar Lisu wadanda suke zaune a wurin su gwanaye ne wajen rera waka da yin raye-raye, babu wani abu da zai iya maye gurbin rera waka a cikin zaman rayuwarsu.

Wakar da kuke saurara waka ce ta gargajiya ta kabilar Lisu, wadda ta burge jama'a kwarai da gaske. 'Yan kabilar Lisu suna da nasu wakokin gargajiya iri daban-daban, maza da mata, tsoffi da kanana dukkansu suna iya rera wakokin. Duk yayin yin muhimman bukukuwa, 'yan kabilar Lisu su kan taru domin rera waka, ana kiran irin wannan bikin gargajiya na rera waka "Baishi". Kwararre Hu Acai wanda ya shafe shekara da shekaru yana nazarin al'adun gargajiyar kabilar Lisu na kwamitin nazarin kabilar Lisu na kungiyar kananan kabilu ta lardin Yunnan ya bayyana cewa: "'Baishi' wani irin salo ne na rera waka wanda ke hadawa da mutane da dama. Yayin da 'yan kabilar Lisu ke bukukuwan taya murnar sallar bazara, dubun-dubatar mutane sun kan taru suna rera wakoki."

1 2 3