Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-21 15:48:15    
Kallon furanni tare da shan ti a lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing

cri

A yayin bikin kallon furannin peach da ake yi a lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing a wannan shekara, an gudanar da jerin harkokin al'adu da abin ya shafa. Bikin murnar cika shekaru 25 da kafuwar dakin tunawa da Cao Xueqing ya kasance daya daga cikin wadannan harkoki. Cao Xueqin, wani shahararren marubuci ne mai girma a kasar Sin. Kagaggen littafi mai suna 'Mafarki na ginin ja' da ya rubuta ya yi shekaru fiye da dari 2 yana samun karbuwa a gida da wajen kasar Sin. Saboda a lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing, an gano takardun musamman da aka manna a gefunan kofa, da abokinsa ya ba shi a matsayin abin kyauta, shi ya sa a shekarar 1984, an gina dakin tunawa da Cao Xueqin a wannan lambun zamani. Yanzu an kebe dakin shan ti a wannan dakin tunawa, inda kuma ake yin wasan kwaikwayo da nune-nune kan al'adun ti da aka tanada cikin kagaggen littafi mai suna 'mafarki na jan babban gida'. Masu yawon shakatawa suna iya shan ti cikin kwanciyar hankali da kuma kara samun fahimta kan al'adun ti a cikin wannan kagaggen littafi. Li Mingxin, shugaban dakin tunawa da Cao Xueqin ya gaya mana cewa, ?A cikin wannan kagaggen littafi, an sha ambata ti. Al'adun ti na da muhimmanci kan nuna dangantaka a tsakanin mutane da kuma abubuwan da ke cikin tunaninsu. Cao Xueqin ya san ti sosai. Ya san ruwan da ya fi dacewa wajen shan ti. Dakin shan ti mai suna 'Xue Qin' da muka kebe ya hada al'adun ti da ilmin kagaggen littafin 'mafarki na jan babban gida' tare, bisa halin musamman da dakin tunawa da Cao Xueqing yake da shi ta fuskar al'adu. Ta haka mutane suna iya shan ti cikin kwanciyar hankali da kuma farin ciki. Wannan yana samun karbuwa a yanzu.?

Domin taimakawa matafiya yin yawo, lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing ya fara jagorantar matafiya ta hanyar wayar salula ba tare da samun kudi ba. Mutane suna iya samun gabatarwa kan wurare masu ni'ima da ilmin tsire-tsire da taswira, muddin sun sami wani shirin wayar salula daga internet ko kuma ta hanyar baza bayanai ta zamani wato bluetooth. Sa'an nan kuma, an tsara wannan shirin wayar salula a Turance da kuma Sinanci. An kuma bambanta wannan shiri bisa nau'o'in wayar salula domin samar wa matafiya sauki.

Masu sauraro, ko kun sami karin fahimta kan lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing bisa shirinmu na yau? Muna maraba da ku zuwa wannan lambun zamani domin kallon furanni masu kyan gani da kuma shan ti mai dadi.


1 2 3