Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-21 15:48:15    
Kallon furanni tare da shan ti a lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing

cri

A yayin bikin, za a nuna furanni da dama da suka shahara a duniya. Alal misali, a kwanaki 10 na tsakiyar watan Afrilu, dimbin furannin tulip kan cika idon matafiya. Mr. Zhao Shiwei ya yi bayani da cewa, yanzu a lambunsu, ana iya ganin shahararrun furanni da yawa da ba a taba ganin irinsu ba a da. Inda ya ce,?A shekarun baya, furannin da jijiyarsu ke da siffar da'ira kan samu rinjaye a yayin bukukuwan da muka shirya, kamar furannin tulip. Mun ajiye furannin tulip masu launuka daban daban a gindin dogayen itatuwa a lambunmu. Wannan yana da kyan gani matuka. Sa'an nan kuma, muna da sauran irin wadannan furannin da jijiyarsu ke da siffar da'ira, wadanda ba safai a kan gani kullum a nan Beijing ba.?

Baya ga furannin tulip, dimbin shahararrun furanni na duniya sun bullo a gida mai dumi da ke cikin lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing. Wannan lambu na rani ya fi girma a duk fadin Asiya. Kazalika kuma, akwai furanni da dama da kasashen waje suka mayar da su a matsayin furen kasa, kamar furanni na kasashen Zambia da Laos da San Marino. Furanni masu ban mamaki da ake reno a lambu na rani sun jawo hankalin dimbin matafiya. Madam Pan ta gaya mana cewa, furen da ta fi so shi ne orchid da ya yi kama da yin rawa. Tana mai cewar,?Yau na kawo ziyara a babban lambun rani a lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing, inda nake ganin kyawawan furanni da yawa. Ban taba ganin furanni masu yawan haka ba. Ga furannin orchid masu yawa. Na fi son furen orchid din da ya yi kama da ana yin rawa. Wannan fure ya yi kama da wata budurwa da ke yin raye-raye. Yana da kyan gani kwarai da gaske. Akwai sauran nau'o'in furannin orchid da itatuwa iri daban daban da kuma karamin kungurmin daji. Dukkansu ina sonsu kwarai.?

Kazalika kuma, a wannan gida mai dumi, ana nuna tsire-tsire masu ban mamaki. Alal misali, muna iya ganin iri mafi girma a duniya wato Double Coconut ko Seychelles Nut a Turance a nan. Mazauna wurin suna kiransa ''ya'yan so'. Wang Mengmeng, mai jagorantar matafiya a lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing ta yi mana bayani da cewa,?Muna ajiye tsire-tsire masu ban mamaki da yawa a wannan yankin nune-nune. Kamar shi iri mafi girma a duniya wato Double Coconut ko Seychelles Nut a Turance. An samo shi ne a tsibirai na kasar Seychelles a tekun Indiya. A duk shekara, ana iya samun irin wannan Seychelles Nut guda 1200 ne kawai a duk fadin duniya. Bayan shekaru 20 zuwa 40, Seychelles Nut za su iya baza furanni, sa'an nan sun huda kuma su yi 'ya'ya. Halin musamman mafi girma na wannan iri mai ban mamaki shi ne ya yi kama da al'aurar mutum sosai. Shi ya sa wani suna na daban da ake kiransa shi ne coconut din da ya yi kama da al'aurar mutum. Ban da wannan kuma, furannin da aka samu daga wannan iri suna yin kama da kayan jiki na haihuwa na namiji da na mace.?

1 2 3