Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-08 20:52:23    
'Yan wasan kwallon tebur sabbin jini na kasar Sin sun fara yin fintikau a cikin gasar tace wadanda za su je Yokohama

cri

Zhang Chao mai shekaru 27 da haihuwa ya kasance cikin kungiyar kasar Sin maza har na tsawon shekaru kusan 10, amma bai taba samun maki mai kyau ba. Duk da haka a kusan karshen kasancewarsa a matsayin dan wasan kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin maza, ba zato ba tsammani ya samu daukaka, kuma a karo na farko ya shiga jerin muhimman 'yan wasan da suke taka muhimmiyar rawa a cikin kungiyar kasar Sin. A ganin wasu, ko da yake ya sami damar shiga gasar fid da gwani ta duniya a wannan karo, amma mai yiwuwa ne ba zai iya samun maki mai kyau a birnin Yokohama ba a sakamakon shekarunsa. Duk da haka, Zhang Chao shi kansa ba ya ganin haka, ya ce,"Yanzu na sami damar shiga gasar a tsakanin namiji da namiji, ba na son bai wa wasu wannan dama. Ko da yake na fi abokan kungiyata tsufa kadan, su samari ne masu karfi, amma tsohon hannu na da fifiko irin nasa. A birnin Yokohama, zan rubanya kokarina domin magance rashin samun sakamako mai kyau da kuma yin da-na-sani a raina a matsayin mamban kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin."

Liu Guoliang, babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin maza ya yi bayani da cewa, sakamako mai ban mamaki da aka samu a yayin gasar tace wadanda za su shiga gasar fid da gwani ta duniya ya shaida cewa, kungiyoyin kasar Sin maza da mata suna da isassun 'yan wasa masu karfi. Irin wannan takara mai zafi a cikin kungiyar kasar Sin tana amfanawa wajen kyautata karfin dukkan 'yan wasa. Inda Mr. Liu ya ce,"Mun cimma burinmu bisa sakamakon da muka samu. A matsayina na babban malamin horas da wasanni, babu shakka ina fatan sabbin jini za su iya nuna gwanintarsu. In tsoffin hannu suka samu damar shiga wasu muhimman gasanni, wannan ba ya da kyau a gare mu ko kadan. Ina fatan sabbin jini za su iya maye gurbin tsoffin hannu cikin sauri. Wannan zai karfafa gwiwar tsoffin hannu da kuma wadanda suke da muhimmiyar rawa a kungiyarmu."

'Yan wasan Wang Liqin da Ma Lin da muka ambata a baya da kuma 'yar wasa Li Xiaoxia da ta zama ta farko a cikin gasar cin kofin duniya a shekarar 2008, da kuma Guo Yan, wata shahararriyar 'yar wasa ta daban ta kasar Sin ba su nuna gwanintarsu yadda ya kamata ba a yayin gasar tace wadanda za su shiga gasar fid da gwani ta duniya, suna matsayin tsakiya. Ko za su iya bullowa a yayin gasar fid da gwani ta duniya da za a yi a birnin Yokohama? Makin da za su samu a yayin wata gasa ta daban a cikin kungiyar kasar Sin da kuma sakamakon da za su samu a yayin aikin horaswa da kungiyar kasar Sin za ta yi a asirce za su yanke hukunci kan makomarsu.


1 2 3