Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-08 20:52:23    
'Yan wasan kwallon tebur sabbin jini na kasar Sin sun fara yin fintikau a cikin gasar tace wadanda za su je Yokohama

cri

Bayan fafatawa mai zafi, Wang Hao da Zhang Chao da kuma Xu Xin sun zama kan gaba a cikin kungiyar kasar Sin maza, yayin da Ding Ning da Zhang Yining da kuma Guo Yue suka kasance kan gaba a tsakanin mata. Wadannan 'yan wasa 6 sun sami tikitocin jirgin sama na zuwa birnin Yokohama. Abin da ya fi burge mutane a yayin wannan gasa shi ne sabbin jini ko kuma wadanda ba a san su sosai ba sun fafata sosai da tsoffin hannu ko kuma muhimman 'yan wasa da suke taka muhimmiyar rawa a cikin kungiyar kasar Sin. Alal misali, 'yar wasa Ding Ning mai shekaru 19 da haihuwa ta rubanya kokarinta ta lashe Zhang Yining, wadda ta zama zakara a cikin gasar wasannin Olympic. Wannan budurwa ta zama ta farko a cikin wannan gasar tacewa. Bayan gasar, Ding Ning ta gaya wa wakilinmu cewa,"Zan shiga gasar fid da gwani ta duniya da za a yi a birnin Yokohama ne da zummar yin koyi da saura da kuma yin gwagwarmaya. Burina na farko shi ne neman lashe 'yan wasan kasashen waje da zan gamu da su. "

Shi Zhihao, babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin mata yana ganin cewa, Ding Ning mai ci gaban fasaha sannu a hankali, wadda ta kan rike dan allon buga kwallon tebur a hannunta na hagu, ita ce sabuwar tauraruwa ta kungiyar kasar Sin da ta fara haskawa. Mr. Shi ya kuma nuna fatansa kan Ding Ning, inda ya ce,"A ganina, makin da Ding Ning ta samu ya faranta rayukan mutane sosai. Wannan ya shaida cewa, akwai sabbin jini a cikin kungiyar kasar Sin mata. Ya kamata ta kara zagewa don samun maki mai kyau. Yanzu Ding Ning ba ta iya tabbatar da samun nasara a cikin fafatawa a tsakaninta da 'yan wasan da suka kware wajen kare harin da ake kai musu ba. A cikin wasu gasanni 2 da aka yi a farkon rabin wannan shekara, ta sha kaye a yayin fafatawar da ta yi da wadanda suka kware wajen mayar da harin da aka kai musu. Na yi imani da cewa, za ta yi karawa da irin wadannan 'yan wasa a cikin gasar fid da gwai ta duniya. Shi ya sa a lokacin da take share fagen gasar, kamata ya yi ta sami babban ci gaba a fannin yin karawa da 'yan wasan da suka kware wajen kare harin da aka kai musu. Ta haka za ta iya zama muhimmiyar 'yar wasa da take da muhimmiyar rawa a cikin kungiyar kasar Sin mata."

In an kwatanta da kungiyar kasar Sin mata, gasar da aka yi a tsakanin kungiyar kasar Sin maza na da sarkakiya matuka. Tsohon hannu Zhang Chao da ya dade yana shan kaye da kuma sabon jini Xu Xin sun samu damar zuwa birnin Yokohama kai tsaye. Irin wannan sakamako ya ba Liu Guoliang, babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin maza mamaki matuka. Musamman ma tsohon hannu Zhang Chao ya ba dukkan kungiyar kasar Sin maza mamaki kwarai da gaske.

1 2 3