Gwamnatinmu a kai a kai ne ta gane abin da ke kasancewa yanzu, bayan da aka mayar da fasahar Yimakan bisa matsayin kayayyakin tarihi na al'adu ba kayayyaki ba a kasar Sin, sai hukumar da abin ya shafa ta tsara matakai da hanyoyin da za a bi don yada fasahar.
Amma, mataimakin shugaban birnin Tongjiang mr You Lijun ya bayyana cewa, wajen kabilar da ke da mutane kadan, kwararru da masana sun riga sun shiga ayyukan ceton fasahar Yimakan da kare ta , amma wannan bai isa ba, ya kamata za a yada ta a tsakanin jama'a. Mr Yu Lijun ya bayyana cewa, Abu mai muhimmanci shi ne yin gado da yadada al'adun kabilar. Ana yada al'adun kabilar a inda 'yan kabilar suke zaman rayuwa, ta hakan, za a iya yada da gadon fasahar a tsakanin jama'a.
Saboda haka gwamnatin wurin ta tsara shiri da kuma shirya ayyukan al'adun da ke da halayen musamman na kabilar, dadin dadawa kuma ta ware kudaden musamman ga wadanda suka yi gadon fasaha don yada fashar ta hanyarsu ta kansu.(Halima) 1 2 3
|