Amma, yanzu ba su da yawa da suka iya rera wakar Yimakan, Malam Wu Liangui yana daya daga cikin wadanda suke iya rera irin wannan waka. Bayan mutuwarsa, sai jikansa mai suna Wu Baochen ya gaji fasahar, ya bayyana cewa, A bakin kogin Helongjiang, da akwai wani tsohon garin da ake kira "Jiejunkou", muna kan hawan tsaunin da ke gabashin garin, muna rera waka , muna fuskantar inda rana take fitowa.
To yanzu za mu sanya muku wata wakar da ke da lakabi haka: wakar jiragen ruwa da ke zirga-zirga a Kogin Wusuli. To ga ta: wata Magana da ta sifanta zaman rayuwar 'yan kabilar Hezhe cewa, an dinki riguna da fatun kifaye, kuma an zuba giya a kasaa don nuna girmama ga aljannu, 'yan kabilar Hezhe sun yi amfani da karnuka don jan keke a kan kankara. 'yan kabilar Hezhe sun yi wa fatun manyan kifaye dukanci , har ma sun yi taushi sosai tamkar yadda zawwati, sa'annan kuma sun yi amfani da su don dinki tufaffi. Yanzu, ba a iya samun wanda yake sanya rigunan fatun kifaye ba, an riga an tanada irin wadannan riguna a cikin gidan baje kolin kayayyakin tarihi,, amma ba su manta fasahar Yimakan ba, bayan aikin da suka yi a rana, sai suka taru a wani wuri daya suka rera wakar Yimakan suna jin nishadi sosai. Mr Wu Baochen ya bayyana cewa,A lokacin da nake karami, bayan dawowar jiragen ruwa masu kamun kifaye, sai yara suka taru a inda jiragen ruwa ke zamewa, suke rera waka a wurin, in ranar bikin kabilar Hezhe ta zo, sai wasu suke raye-raye, wasunsu suke rera wakoki, wasu ma su ke ba da labarai, wasu kuma suke kada kayayyakin kida da aka yi da tsirkiyoyi.
A lokacin ba da dadewa ba, ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta tabbatar da cewa, Mr Wu Baochen shi ne mai gadon fasahar Yimakan bisa matsayin kasa. A ganinsa, fasahar Yimakan ita ce fasaha mai daraja sosai da ke iya wakiltar tarihi da al'adu da al'adar zaman rayuwa da bikin nuna da'a da sauransu na kabilar Hezhe, ya kamata a yada ta daga zuri'a zuwa zuri'a, ya bayyana cewa, Yanzu, ana iya bayyana cewa, fasahar Yimakan ita ce abu mafi daraja ga 'yan kabilar Hezhe, ya kamata mu yada ta daga zuri'a zuwa zuri'a. Wu Baochen shi kansa ya yi iyakacin kokari wajen gadon fasahar Yimakan da yadada ta ba tare da kasala ba. Amma dayake hanyar zaman rayuwa na kabilar Hezhe ya sami sauyawa, shi ya sa fasahar yana fuskantar ricikin mutuwa. Yanzu wadanda suka iya rera wakokin yawansu ya kai biyar kawai. Malam Wu Baochen ya bayyana cewa, Kodayake ina da himma sosai wajen yada fasahar, amma matsalolin da na samu na da yawan gaske, halin da ake ciki kuma ake nuna yabo gare shi ta hanyar fasahar Yimakan ya sami sauyawa, sa'anan kuma kabilar Hezhe ba ta da rubuce-rubuce, shi ya sa yaduwarta na da wuya sosai, saboda haka cetonta da kare ta ayyuka ne da ake yi cikin gaggawa , Mr Wu Baochen ya ci gaba da bayyana cewa,Shekaruna da haihuwa sun riga sun kai 50, wajen al'adun kabilar Hezhe, in ban je koyon al'adun kabilar Hezhe ba, to ban iya fahimtar fasahar ba, balle a ce yaranmu, su ba su fahimci kome da kome dangane da fasahar Yimakan ba.
1 2 3
|