Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-07 22:11:09    
Kyakkyawan babban kwarin kogin Nujiang da ke lardin Yunnan

cri

A can da, a sakamakon manyan tsaunuka masu tsayi da kuma ruwan da ke gangara cikin sauri, ba a iya shimfida gada a tsakanin gabobin kogin Nujiang ba. Mutane sun hada gabobin kogin da wata igiyar karfe domin kaiwa da kawowa. Yanzu mazauna kogin Nujiang da suka taba kaiwa da kawowa a tsakanin gabobin kogin ta hanyar igiyar karfe daga zuriya zuwa zuriya sun raya wannan hanyar zirga-zirga mai hadari zuwa shirin yawon shakatawa na zamani. In kana da karfin zuciya ta rashin tsoro sosai, to, za ka iya wucewa ta kogin Nujiang da wannan igiyar karfe a karkashin jagorancin mazauna wurin. Madam Liu da ta zo daga birnin Beijing tana farin ciki sosai, ta gaya mana cewa,"Ina dan tsoro bayan da na daura bel din kiyaye hadari, amma ban ji tsoro ko kadan ba bayan da na kama hanyata a kan wannan igiyar karfe na tsawon mita fiye da 10, cike nake da murna. A ganina, wannan shirin yawon shakatawa na zamani ya sa ni kara jin dadin zuwana a kogin Nujiang."

Daga ko ina suke, masu yawon shakatawa suna tafiya tare da rakiyar kogin Nujiang. A bangare na sama na kogin, ci gaban ruwan kogin ya samu babban sauyi na ba zata. Kogin Nujiang ya shiga cikin gundumar Bingzhongluo daga kwarin Qiunatong a arewa, ya kuma iso gundumar Dala daga kudancin gundumar Bingzhongluo. A sakamakon wasu kariyar da manyan duwatsu suke samarwa, a gundumar Dala, kogin Nujiang ya bullo da wani sashen bakin kogin, wanda aka kira shi sashen bakin kogin Nujiang mafi muhimmanci. Li Wanlin, wani ma'aikacin kula da wannan sashen bakin kogi ya bayyana cewa,"Halin musamman na wannan sashen bakin kogi shi ne kogin Nujiang ya lankwasa sosai a nan, shi ya sa muka sami wani karamin tsibiri a wurin da kogin ya lankwasa sosai. A wannan tsibiri, ana noman gonaki yadda ya kamata. A safe, a sakamakon gajimare da yawa, kauyuka da gidaje kan boye a cikinsu."

A arewacin gundumar Bingzhongluo, babban tsaunin Gaoligong da babban tsaunin dusar kankara na Biluo da ke tsayawa a gabobin kogin Nujiang sun hadu da juna. Sun samar da babbar kofar dutse mai tsayin mita dari 5 ko fiye da kuma mai fadin mita kusan dari 2. Shi ne Shimenguan, wadda mazauna wurin su kan kira ta "Na Yi Qiang", wato wata babbar tasha ce wadda da wuya sosai ko aljanu su iya wucewa. Mr Li Wanling ya kara da cewa,"Shimenguan tana da girma da kyan gani sosai. Tsayinta ya wuce mita dari 5. Hayi ne suka samar mana Shimenguan. Daga nesa, sai ka ce wata kofar dutse. Shimenguan na da matukar muhimmanci wajen shiga cikin jihar Tibet kamar yadda makogwaro yake da muhimmanci ga ko wane mutum."

A duk fadin yankin kogin Nujiang, an fi samun wurare masu ni'ima a gundumar Bingzhongluo, wadda aka kira ta "wurin da mutane da aljanu suke yin zaman tare cikin lumana". A gaban manyan tsaunukan da dusar kankara kan mamaye a duk shekara, ana yin shuke-shuke na launukan rawaya da kore masu duhu da haske tare da ganin rufi na toka-toka a ciki. Ta haka an iya samun yanayin kwanciyar hankali irin na yankunan karkara tare da ganin hayakin dafa abinci. Mutane masu tarin yawa sun zo nan ne domin nisantar da kansu daga hayaniyar birane da kuma jin dadin kwanciyar hankali a muhalli.

'Yan kananan kabilun wurin kan ba wa baki giyar da suka sarrafa tare da rera waka mai dadin ji domin maraba da bakin da suka zo daga wurare masu nisa da hannu biyu biyu kuma tare da budaddiyar zuciya.

"Takaitacciyar ma'anar wakar ita ce suna yin marhabinku da zuwa nan kogin Nujiang. Suna farin ciki sosai saboda zuwanku a kogin Nujiang, shi ya sa suke wake-wake da raye-raye. Suna sake nuna muku marhabi da zuwanku a kogin Nujiang. Haka kuma, kogin Nujiang ya yi maraba da ku!"


1 2