Abin tunatarwa a nan shi ne da akwai koguna da yawa a nan kasar Sin. Kogin Nujiang wani babban kogi ne da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Lardin Yunnan da kogin ya ratsa wuri ne da aka fi samun yawan 'yan kananan kabilu a kasar Sin. Yau ma bari mu matsa kusa da babban kwarin kogin Nujiang domin bude idonmu a ni'imtattun wuraren da ke gabobin kogin da kuma halayen musamman na al'adun kananan kabilun.
Masu sauraro, abin da kuke saurara a yanzu wakar da 'yan kabilar Lisu suke rerawa ce a cikin harshensu domin nishadin baki. 'Yan kabilar Lisu suna zaune a yankin Nujiang a arewa maso yammacin lardin Yunnan, inda 'yan kabilun Nu da Dulong da Han da Pumi da Yi da Tibet da kuma Dai su ma suke yin zaman tare cikin lumana, wadanda yawan 'yan kananan kabilun ya wuce kashi 90 cikin dari bisa jimilar mazauna yankin.
Fadin yankin Nujiang ya kai misalin murabba'in kilomita dubu 14. Manyan tsaunuka da kuma koguna da dama su ne suka fito da wannan yanki, tamkar dai yankin Nujiang na boye ne a tsakanin manyan tsaunukan, saboda haka mutane ba fahimci irin kayatarwa ta ganin babban kwarin kogin Nujiang sosai ba. Amma a sakamakon kasancewar babban kwarin a yankin karkara, shi ya sa aka iya samun damar ganin ainihin kyansa. Chen Jun, wani mazaunin wurin ya yi mana karin bayani kan garinsa da cewar,"Garina na da kyan gani sosai. Mazauna wurin na da kirki sosai tare da son karbar baki. Kyan ganin garina wani ikon Allah ne."
Ban da wannan kuma, Zhao Wensheng, wanda ke aiki a hukumar yawon shakatawa ta yankin Nujiang yana mai cewar,"Babban kwarin kogin Nujiang ya yi kama da wani littafi mai shafi da yawa da yake iya koya mana ilmin falsafa da ilmin muhalli. In ka kai ziyara a babban kwarin ta hanyoyi daban daban, to, za ka iya samun abubuwa masu nau'o'i daban daban."
A babban kwarin kogin Nujiang, babu shakka yankin yawon shakatawa na Shi Yue Liang wani wuri ne wurin da ya fi nuna mana ikon Allah. A tsakanin manyan tsaunuka na kore mai duhu, daga nesa akwai wani babban kogon dutse ne da ya yi kama da cikakken wata wato Yue Liang a bakin Sinawa da ke kasancewa a sararin sama. A shekarun 1930, wato a yayin da mutanen Sin suka yi yaki da Japanawa mahara, mayakan saman da ke karkashin shugabancin janar C. L. Chennault na kasar Amurka sun taba mayar da wannan kogon dutse na Shi Yue Liang tamkar muhimmiyar alama ce a kan hanyar tafiyarsu a sararin sama a sakamakon rasa jagorar wurare daga kasa. Irin wannan kyakkyawan zumuncin da ke tsakanin Sin da Amurka ya sanya yankin Shi Yue Liang ya kara nuna bambanci da saura.
Kogin Nujiang mai tsawon kilomita fiye da dubu 3 da dari 2 ya sami tushensa ne a babban tsaunin Tang Gu La na kudu, wanda ya ratsa jihar Tibet mai cin gashin kanta da lardin Yunnan da kuma kasar Myanmar, inda ya shiga cikin mashigin Bengal na tekun Indiya. A lokacin hunturu, ruwa kan gangara sannu a hankali a yawancin kogin Nujiang da ke cikin babban kwarin, amma sai a yankin Lao Hu Tiao kawai ruwan yake samun babban sauyi, ya gangara cikin sauri tare da babban amo.
1 2
|