Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-18 10:51:53    
Me ya sa ake ta da zaune tsaye a kasar Madagascar

cri

Na biyu, shugaba Ravalomanana ya kan yi amfani da mukarabinsa, ta yadda ya kan sa sojojin kasar rashin jin dadi. A watan Oktoba na shekarar 2007, shugaba Ravalomanana ya nada Cecile Manorohanta, 'yar gaban goshinsa wadda ba ta da tushe cikin sojoji, zuwa mukamin ministar tsaron kasar, haka kuma a watan Fabarairu na shekarar bana, ya nada Edmond Rasolomahandry a matsayin hafsan hafsoshin sojojin kasar. Abun ya samu kin amincewa daga sojojin kasar sosai, har ma sun ta da bore, sun zabi hafsan hafsoshin da kansu.

Dalili na uku shi ne, sabuwar dokar jam'iyyar siyasa ta sa jam'iyyum wadanda ba su kan kujerar mulki su hada kawunansu. A watan Janairu na shekarar bana, shugaba Ravalomanana ya sa majalisun kasar, inda jam'iyyar TIM da ke kan karagar mulki take da rinjaye, su zartas da kudurin gyara tsarin mulki, da dokar jam'iyyar siyasa. Sa'an nan cikin dokokin, an kayyade cewa, dole ne a shiga zaben kasar bisa matsayin wakilin wata jam'iyya, inda ake da nufin nuna kin amincewa ga Andry Rajoelina, wanda ya ci zabe ya zama magajin birnin Antananarivo,hedikwatar kasar Madagascar, a shekarar 2007, bisa matsayinsa na zaman kansa, inda bai wakilci wata jam'iyya ba. Cikin shekarun da suka wuce, magaji Rajoelina ya samu sabanin ra'ayi da shugaban kasar kan abubuwa da yawa, kamar su raba kayayyakin tallafi, da samar da wutar lantarki da ruwa, da dai sauransu.

1 2 3