Shugaban jihar Tibet, Changba Phuntsog ya bayyana cewa,"Muna kokarin aiwatar da shirin samar da kyawawan gidaje ga jama'a, kuma muna kara raya ayyukan samar da ruwa da wutar lantarki da shimfida hanyoyi da sadarwa da dai sauran manyan ayyuka. Bisa kokarinmu, zaman rayuwar manoma makiyaya ya sami kyautatuwa sosai, har ma manoma makiyaya da yawansu ya kai dubu 860 sun kaura cikin sabbin gidaje masu inganci."
Sonam Dorje, wani tsoho dan shekaru 62 da ke da zama a birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet, ya ce, kullum ya kan taya kansa murnar zaman alheri, ya ce,"Ni ba mai arziki ba a unguwarmu, amma ina da wani kanti. Na kan yi tufafin 'yan kabilar Tibet, yanzu zaman rayuwa ya kyautata ga al'ummar Tibet, shi ya sa su kan sayi sabbin tufafi idan an yi bukukuwa. Iyalina na zama cikin gida da ke da hawa biyu, kuma ba mu damuwa da abinci da abin sanyawa. Kwatankwacin rashin hakkoki a zamanin gargajiya, me ya sa ba zan taya kaina murnar zaman yau?" (Lubabatu) 1 2 3
|