
Tun fil azal, Tibet wani kashi ne na kasar Sin. Bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, a shekarar 1951, gwamnatin kasar Sin da hukumar Tibet sun daddale yarjejeniyar 'yantar da Tibet cikin lumana, kuma bisa halin da Tibet ke ciki a wancan lokaci, ba a gyara tsarin zaman al'umma da na siyasa a wurin ba nan da nan. Amma a watan Maris na shekarar 1959, wasu tsirarrun 'yan koma baya na Tibet da ke karkashin jagorancin Dalai Lama sun ta da bore kan yunkurin kiyaye tsarin mallakar bayi manoma, kuma a yayin da gwamnatin kasar Sin ke kwantar da tawaye, ta kuma fara yin gyaran dimokuradiyya a Tibet, inda aka yi watsi da tsarin mallakar bayi manoma, tare kuma 'yantar da miliyoyin bayi manoma.
Gyare-gyaren dimokuradiyya da aka gudanar a Tibet wani muhimmin al'amari ne daga cikin harkar 'yantar da bayin duniya, haka kuma wani babban ci gaba ne ga hakkin dan Adam na duniya. A zamanin da, kashi 90% na al'ummar Tibet sun kasance bayi manoma, kuma a ganin masu mallakarsu, su abubuwan aiki ne da ke iya magana, kuma ana iya sayar da su yadda aka ga dama, ko kadan ba su da 'yanci. Amma bayan gyare-gyaren, sun sami 'yanci, kuma bisa goyon bayan gwamnatin kasar Sin da na sauran lardunan kasar, sun yi kokarin raya garinsu, ta yadda Tibet ta sami saurin ci gaba ta fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu.
1 2 3
|