Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-02 12:56:46    
Muhimmin nufin taron tattalin arzikin duniya a shekara ta 2009 shi ne hadin kai da yin kwaskwarima

cri

A ran 1 ga watan Fabrairu a birnin Davos aka kammala taron tattalin arziki na duniya da aka sa kwanaki biyar ana yinsa. Wakilai 2500 da suka halarci taron sun yi muhawawarori guda sama da 220 kan batutuwa da dama, sun yi tattaunawa kan matsalar tabarbarewa tattalin arziki da sauran batutuwan da suka shafi duniya baki daya.Muhimmin nufi a wannan taron shi ne a mika tsaye da cikakken imani, da karfafa hadin kai da kuma gyara tsarin kudade na duniya dake kasancewa a halin yanzu.

A cikakken zaman rufe taron, Mr Klaus Schwab wanda ya kirkiro taron tattalin arziki na duniya ya bayyana cewa taron nan ya samar da wani muhimmin sako,shi ne kamata ya yi kasashen duniya su gaggauta su mayar da martani ga wannan matsala da ta fi tsanani tun shekarun 1930. Ya ce "matsalar tabarbarewar tattalin arziki ta bazu ko ina a duniya, matsalar da ta shafi duniya baki daya, kamata ya yi a gabatar da shirin samun bakin zaren warware matsalar na duniya bai daya. Dole ne mu yi tunani kan nan gaba,mu sake tsara tsarin kudaden duniya ta hanyar hadin kai ta yadda zai dace da yanayin da duniya zai shiga bayan warware matsalar tabarbarewar."

A ganin mahalartan taron, ya kamata a binciki halin da duniya ke ciki a yanzu cikin nutuwa. A wasu lokuta na nan gaba,makomar tattalin arzikin duniya tana cikin dusashewa. Marasa aikin yi na ci gaba da karuwa, masana'antu na rufe kofofinsu, matsalar talauci ta kara tsanani. Kan wadannan matsalolin, an zartas da manufofin hadin kai gudad biyar a gun taron na cewa na farko a goyi bayan gwamnatocin kasa da kasa da kungiyoyin duniya kamar kungiyar kasashe 20 su kara taka rawa wajen warware matsalar tabarbarewar tattalin arzikin duniya; na biyu yayin da ake tinkarar matsalar kudade, ya kamata a dora muhimmanci kan kalubalen duniya kamar dumamar yanayi da karancin ruwa; na uku a kaddamar da yunkurin gyara shiri da tsarin hadin kai na duniya dake a kwai a halin yanzu; na hudu a sa kaimi wajen mai da masana'antu a matsayin manbobi mau daukar nauyin zamantakewa;na biyar a karfafa kwarin gwiwar tattalin arzikin duniya.

1 2