Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-02 12:56:46    
Muhimmin nufin taron tattalin arzikin duniya a shekara ta 2009 shi ne hadin kai da yin kwaskwarima

cri

An kira wannan taron shekara shekara na tattalin arzikin duniya birnin Davos ne yayin da matsalar tabarbarewar tattalin arziki ke kara tsananni da koma bayan tattalin arziki na manyan kungiyoyin kasashen yamma da bacin rai ya game duniya. Shi ya sa ya dauki hankalin kasashe da kungiyoyi na duniya, da haka wannan taron ya zama wani batu mafi muhimmanci tun bayan kafuwarsa a cikin shekarun kimanin 40. firayim minista sama da 40 sun shiga taron nan, adadinsu ya karu da ninki daya bisa na shekarun baya bayan nan ciki har da firayim minista na kasar Sin Wen Jiabao da takwarorinsa na kasar Rasha Vladimir Putin da shugabar gwamnatin Jamus Ange;a Merkel, da firayim ministan Britaniya Gordon Brown da takwaransa na kasar Japan Taro Aso. Har ma babban sakatare na majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon da da kuma babban sakataren kungiyar ciniki ta duniya Pascal Lamy da shugabanni na sauran kungiyoyi fiye da talatin na duniya sun shiga taron, sun yi tattaunawa tare da mahalartan taron kan yadda za a tinkari matsalar tabarbarewar tattalin arzikin duniya, a sa'I daya kuma sun sa lura kan wasu muhimman batutuwa na duniya kamar su dumamar yanayi da tsaron makamashi da abinci da ruwa da kuma batun kan halin da gabas ta tsakiya ke ciki.

A cikin jawabansu a gun taron,an fi mayar da hankali kan kalmar "a mika tsaye tare da cikakken imani."Firayim ministan kasar Sin ya yi jawabi wanda ya ke da lakabi haka;" A karkafa kwarin gwiwa da hadin kai wajen ciyar da tattalin arzikin duniya gaba",jawabinsa ya samu karbuwa a mahalartan taron. A ganin mahalartan taron,da ya ke duniya ke fama da tabarbarewar tattalin arziki,gwamnatin kasar Sin ta dauki tsauraran matakai wajen tinkarar matsala,har ta sami nasara. Kasar Sin za ta ba da karin taimako wajen bunkasa tattalin arzikinta da kuma farfado da tattalin arzikin duniya. (Ali)


1 2