Asha-Rose Migiro, mataimakiyar sakataren janar na MDD ta yi jawabi a wajen taron, inda ta jaddada cewa, dole ne, a aiwatar da aikin agaji lami lafiya, ta yadda za a taimaki mutanen Gaza da ke cikin tsananin karanci. Haka zalika ta nuna cewa, don cimma tsagaita bude wuta mai dorewa, kamata ya yi, a dau matakai don hana fasa kwaurin makamai zuwa zirin Gaza, da sake bude kwastam da ke kan iyakar kasa, da kuma dinke zirin Gaza da gabar yamma ta kogin Jordan tare, bisa jagorar da gwamnatin halal ta yi.
Riyad Mansour, dan kallon Falasdinawa da ke MDD ya ce, har yanzu jama'ar Falasdinu na dogaro kan gamayyar kasa da kasa da ta gaggauta cimma tsagaita bude wuta, da kawo karshen kisan kiyashi da munanan ayyuka marasa adalci da sojojin Isra'ila suka yi wa Falasdinawa. Haka kuma, ya sake kira ga bangaren Isra'ila da ya soke kangiya maras adalci da ya yi wa zirin Gaza, da bude kwastam da ke kan iyakar kasa, ta yadda za a tabbatar da cewa, kayan agaji da masu ba da taimakon jin kai za su shiga cikin zirin Gaza ba tare da shinge ba.
Abelardo Moreno, wakilin Cuba da ke MDD, ya yi jawabi a madadin kungiyar 'yan ba ruwanmu, inda ya la'anci Isra'ila da tsattsauran harshe, kan kutsa kai da ta yi wa Falasdinu, da kunnen uwar shegu da ta yi wa kudurin MDD. Mista Moreno ya bukaci Isra'ila da ta dau takamaiman mataki nan take, ta koma ga yadda kudurin MDD ke tanadar. Haka zalika, Mista Moreno ya yi ta'aziyya ga Falasdinawa farar hula da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren sojojin Isra'ila, da nuna damuwa kan matsalolin da likitoci da masu ba da agaji suka gamu da su yayin da suke kubutar da jama'ar Falasdinu.(Bello Wang) 1 2
|