Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-16 15:51:36    
MDD ta kira taron gaggawa don tattauna kan halin da ake ciki a zirin Gaza

cri

Cikin shirin yau za mu yi muku bayani kan taron musamman da MDD ta kira don sassanta mawuyacin halin da zirin Gaza ke ciki, yayin da dakarun Isra'ila ke cigaba da kutsawa cikin zirin.

Bisa halin da ake ciki ne, babban taron MDD na 63 ya yi zamansa na musamman a ran 15 ga watan Janairu, inda jami'an kasa da kasa suka tattauna kan yadda za a samu bakin zaren warware matsalar. A wajen taron, Miguel Brockmann, shugaban babban taron MDD ya yi jawabi, inda ya yi kira da kasashen duniya da su zartas da wani kuduri, don kawo karshen zubar da jini a zirin Gaza,

Da ma kafin a kira taron, kasar Isra'ila ta nuna shakka kan ko ana bukatar kira taron, domin kwamitin sulhu na MDD ya riga ya dau matakai kan rikicin zirin Gaza, kana Ban Ki-moon, sakataen janar na Majalisar shi ma yana rangadi a gabas ta tsakiya don sassanta rikicin. Dangane da shakkar da Isra'ila ta nuna, Mista Brockmann ya mayar da martani da cewa, an jima kafin Ban Ki-Moon da ministan harkokin wajen kasar Isra'ila su kira taron manema labaru, jiragen saman yaki na Isra'ila sun sake kai harin bomabomai kan harabar MDD dake Gaza. A hakika, bangaren Isra'ila ya yi wa kudurin MDD kunnen uwar shegu, shi ya sa ya zama wajibi a kira taron gaggawa a MDD.

Cikin jawabinsa, Mista Brockmann ya kara da cewa, hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai wa makarantu, da gidajen farar hula, da masallatai, da kuma harabar MDD sun haddasa rasa rayukan mutane fiye da dubu, da kawo hasarar dukiyoyi da yawa. Abin da sojojin Isra'ila suka yi, ya karya dokar kasa da kasa da kuma haddasa mummunan rikicin jin kai. Mista Brockmann ya ce, maganar da shugaban kasar Isra'ila ya yi ta kin yarda da kudurin MDD da cigaba da hare-haren, na nuna fatali da MDD da dokar kasa da kasa.


1 2