Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-06 17:31:19    
Shigad da sabbin fasahohin zamani cikin zaman jama'a

cri

A gun wannan taron cinikayya, ana iya samun dimbin sakamako masu kyau da aka samu daga wajen sabbin fasahohin zamani da ake iya yin amfani da su a cikin zaman jama'a kamar littafin nuna fasahar kide-kide da ke yin amfani da wutar lantarki. Kuma A kan kira taron da kasar Sin ta kan shirya a ko wace shekara daga shekara ta 1999 "bikin nune-nune na farko na kimiyya da fasaha na kasar Sin", kuma an mayar da "kimiyya da fasaha ke iya kyautata zaman jama'a, kirkire-kirkire ke iya canja duniya" a matsayin babban take na taron na wannan karo. Sabo da haka, ana iya samun dimbin kayayyakin zamani da ke da nasaba da zaman jama'a na yau da kullum.

A gaban dakalin nuna talibijin na kamfanin KONKA, wani akwatin talibijin mai ban sha'awa ya jawo hankalin masu kallo da yawa. Kuma wakilinmu ya gano cewa, bayan da wani dan kallo ya sanya safar hannu ta musamman, lokacin da ya kada hannunsa, sai hanyoyin talibijin suka canja, kuma lokacin da ya juya hannunsa, sai yawan muryar talibijin ya canja. Mr. Wang na kamfanin KONKA ya gaya mana cewa, dalilin da ya sa aka raya irin wannan kaya shi ne domin masu yin amfani da talibijin za su iya kara jin dadin amfani da talibijin. Kuma ya kara da cewa, "A ganina, matasa za su nuna sha'awa ga irin wannan talibijin. Yanzu ana iya samun dimbin wasanni da ke iya motsa jiki, sabo da haka muna tsai da kudurin kera irin wannan talibijin da ke iya biya bukatun rukunonin mutane daban daban."

Ban da wannan kuma, wasu 'yan kallo suna ganin cewa, lallai bunkasuwar kimiyya da fasaha ta canja zaman dan Adam sosai. (Kande Gao)


1 2