A kwanan nan, an kira taron cinikayya a karo na 10 tsakanin kasa da kasa na kasar Sin kan kyakkyawan sakamakon da aka samu daga wajen sabbin fasahohin zamani a birnin Shenzhen da ke kudancin kasar Sin, inda aka nuna dimbin kayayyaki na sabbin fasahohin zamani da ke da nasaba da zaman jama'a. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu leka wannan taron cinikayya domin jin dadin sabbin fasahohin zamani tare.
A cikin wani dakin nune-nune na taron cinikayya kan kyakkyawan sakamakon da aka samu daga wajen sabbin fasahohin zamani, wata kungiyar makada ta gargajiya da ta kunshe da mutane goma suna nuna fasahar kide-kide. Amma abin da ya sha bamban shi ne an samu wani allon nuna bayanai na LCD da ke gaban ko wane makadi a maimakon littafin nuna fasahar kide-kide da a kan gani kullum. Fan Zuyin, babban malami na kwalejin koyon ilmin kide-kide ta kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, littafin nuna fasahar kide-kide kaya ne da ba a iya raba shi da makada ba. Amma lokacin da suke nuna fasahar kide-kide, makada su kan fuskanci wata matsala, wato suna bukatar juya shafuffukan littafin bisa lokaci-lokaci. Amma irin wannan littafin nuna fasahar kide-kide da ke iya amfani da wutar lantarki da aka nuna a gun taron cinikayya ya warware matsalar, wato ya iya juya shafuffukansa da kansa. Kuma Mr. Fan ya ce, "Har kullum ana yin nazari kan littafin nuna fasahar kide-kide da ke yin amfani da wutar lantarki a duniya, amma bai samu nasara ba. A kasar Sin kuma kungiyoyin makada sun riga sun fara yin amfani da irin wannan littafin nuna fasahar kide-kide da Sin ta kera, sabo da haka muna kan gaba a wannan fanni a duniya."
1 2
|