A gun taron tattaunawa kuma Hu Jintao ya gabatar da muhimman ra'ayoyi guda 6 don sa kaimi ga bunkasa dangantakar da ke tsakanin gabobin 2 cikin lumana.
A yayin da Mr. Hu Jintao ya tabo magana kan matsalar sa aya ga yin gaba da juna tsakanin gabobi 2 ya ce, "Hakan yana da amfani ga tsara shirin yin shawarwari tsakanin gabobin 2 da yin mu'amala tsakaninsu, gabobin 2 kuma za su iya tattauna hakikanan batutuwa kan dangantakar siyasa bisa halin musamman da ake ciki wato ba a samun dinkuwar kasa daya ba tukuna."
Lokacin da Hu Jintao ya tabo magana kan matsalar cuku-cukun da hukumar Taiwan ke yi domin neman shiga kungiyoyin kasashen duniya ya ce, "A kauce hanyar yin wasu ayyukan da ba tilas ga yin su ba a gabobin 2 kan harkokin kasashen duniya, wannan yana da amfani ga samun moriyar tarayya ga dukkan al'ummar kasar Sin baki daya. Kuma in da bukata za a iya kara yin shawarwari kan makomar yin mu'amalar da hukumar Taiwan ke yi a tsakaninta da mutane ko kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen waje wajen tattalin arziki da al'adu, kan matsalar neman shiga ayyukan kungiyoyin kasashen duniya da hukumar Taiwan ke yi, ya kamata ta yi su ne bisa sharadin farko na rishin kawo "kasar Sin 2 ko Sin daya Taiwan daya". Tabbatar da samun dinkuwar kasa daya harkokin gida ne zalla na kasar Sin, kada sauran kasashe su sa hannu a ciki".(Umaru) 1 2
|