A ran 31 ga wata an yi taron tattaunawa a nan birnin Beijing domin tunawa da ranar cikon shekaru 30 da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta bayar da "takardar bayani ga 'yanuwa na Taiwan", a gun taron Mr. Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban kasar Sin ya gabatar da muhimman ra'ayoyi guda 6 don sa kaimi ga bunkasa dangantakar da ke tsakanin gabobin 2 cikin lumana.
A ran 1 ga watan Janairu na shekarar 1979, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta bayar da "takardar bayani ga 'yanuwa na Taiwan", wadda a ciki ta ba da shawara cewa, za a kawo karshe ga yin gaba da juna wajen sha'anin soja tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan ta hanyar yin shawarwari, ta yadda za a tabbatar da yin mu'amala daga fannoni 3 wato sadarwa da zirga-zirgar jiragen sama da ciniki a tsakaninsu.
Cikin shekaru 30 da suka wce, kuma bisa kokarin da mutanen sassa daban-daban na gabobi 2 suka yi tare, an samu manyan sauye- sauye wajen dangantakar da ke tsakanin gabobin 2.
A gun taron tattaunawa da aka yi a wannan rana, Hu Jintao ya bayyana cewa, "Don sa kaimi ga ciyar da dangantakar tsakanin gabobin 2 gaba, da tabbatar da samun dinkuwar kasar mahaifa daya, abu mafi muhimmanci da ya kamata a yi shi ne, bin ka'idar "samun dinkuwar kasa daya cikin lumana, da kasa daya mai tsarin mulki 2", da ra'ayoyi guda 8 dangane da bunkasa dangantakar tsakanin gabobin 2 a halin yanzu, da daukaka ci gaban aikin samun dinkuwar kasar mahaifa daya cikin lumana, a tsaya haikan kan ka'idar kasar Sin daya kawai a duniya, da yin matukar kokari don neman samun dinkuwar kasar daya, da kafa fata kan jama'ar Taiwan, da yin adawa da danyen aiki da ake yi domin kawo baraka ga Taiwan, a tsaya haikan kan wadannan ayyuka ba tare da kasala ba."
1 2
|