Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-18 20:11:19    
Tilas ne Sin ta ci gaba da yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da kuma raya hanyar gurguza ta zamani, in ji shugaban kasar

cri

 

A cikin jawabinsa, Mr.Hu Jintao ya yi nuni da cewa, nasarorin da Sin ta cimma a cikin shekaru 30 da suka gabata sun nuna cewa, yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje muhimmin zabi ne ga kasar Sin, haka kuma hanya ce da tilas ne a bi domin bunkasa harkokin gurguza da ke da sigar musamman ta kasar Sin da kuma farfado da al'ummar kasar. Ya ce,"yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje ya cimma burin jam'iyyar kwaminis ta Sin da na jama'ar kasar, ba za a iya musanta nasarorin da aka cimma sakamakon manufar ba, kuma babu wata mafita ta daban idan an dakatar da ita."

A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin na kan mataki na farko wajen bunkasa harkokin gurguzu, kuma za ta dade tana kan matakin. Sabo da haka, tana ci gaba da fuskantar dimbin matsaloli, ga shi kuma matsalar kudi ta duniya ta kawo wa tattalin arzikin kasar Sin illolin da ba za a iya dauke kai a gare su ba. A game da wannan, Mr.Hu Jintao ya ce,"A halin da duniya ke ciki yanzu, musamman ma a yayin da matsalar kudi ke dinga yaduwa a duniya, kamata ya yi mu kara dora muhimmanci a kan bunkasa tattalin arziki ba tare da sauyawa ba, mu samu arziki da cigaba ba tare da gurbata muhalli ba. Sa'an nan, ya kamata mu tabbatar da matakai daban daban na kara bunkasa bukatun gida da bunkasa tattalin arziki, ta yadda tattalin arziki zai iya bunkasa cikin inganci da kuma sauri. Ban da wannan, ya kamata mu inganta bude kofa ga kasashen waje, mu kyautata hadin gwiwar da ke tsakaninmu da kasashen waje, ta yadda za mu sa kaimi ga kasashe daban daban su samu ci gaba tare bisa bunkasuwarmu cikin lumana." (Lubabatu)


1 2