Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-18 20:11:19    
Tilas ne Sin ta ci gaba da yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da kuma raya hanyar gurguza ta zamani, in ji shugaban kasar

cri

Tun daga ran 18 zuwa ran 22 ga watan Disamba na shekarar 1978, an gudanar da cikakken zama na uku na kwamitin tsakiya na 11 na jam'iyyar kwaminis ta Sin a birnin Beijing. A gun wannan taro mai matukar muhimmanci a tarihin jam'iyyar kwaminis ta Sin, an gabatar da sabuwar hanyar gurguzu da ke da sigar musamman ta kasar Sin, wadda kuma ta bude wani sabon babin da ake yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje. A cikin shekaru 30 daga bisani, kasar Sin ta sami manyan nasarori a wajen bunkasa harkoki daban daban. Yau a nan birnin Beijing, an kira taron tunawa da cika shekaru 30 da gudanar da cikakken zama na uku na kwamitin tsakiya na 11 na jam'iyyar kwaminis ta Sin, inda Mr.Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin ya yi nuni da cewa, yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da Sin ke yi ta cimma burin jama'a, kuma ya biya bukatun zamani. Babu wata mafita ta daban, tilas ne Sin ta ci gaba da kiyaye manufar.

A gun taron, Mr. Hu Jintao ya yi jawabi, inda ya nuna babban yabo ga taron da aka kira yau da shekaru 30 da suka gabata. Ya ce,"A ran 18 ga watan Disamba na shekarar 1978, wato daidai rana irin ta yau a shekaru 30 da suka gabata, an kira cikakken taro na uku na kwamitin tsakiya na 11 na jam'iyyar kwaminis ta Sin. Taron dai ya kasance wani babban abu a tarihin jam'iyyar kwaminis ta Sin tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, wanda kuma ya bude wani sabon babi na yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje."

Manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje ta kawo wa kasar Sin manyan nasarorin da suka burge duniya kwarai da gaske. A cikin shekaru 30 da suka gabata, yawan GDP na kasar Sin ya yi ta karuwa da kusan kashi 10% a kowace shekara, kuma matsayin tattalin arzikinta ya dagu har ya zama na hudu a duniya. A cikin shekarun nan 30, yawan kudaden shiga da jama'ar kasar Sin suka samu ya yi ta saurin karuwa, wato matsakaicin kudaden da mazauna birane da garuruwa na kasar Sin suke iya kashewa ya karu daga yuan 343 zuwa 13786, sa'an nan, yawan mazauna kauyuka da ke fama da talauci ya ragu daga miliyan 250 zuwa miliyan 14.


1 2