Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-16 15:52:04    
Bush ya ziyarci Afghanistan ba zato ba tsammani

cri

Bugu da kari kuma, Mr. Bush ya yi yunkurin ci gaba da kalubalantar kasar Pakistan kan inganta yaki da ta'addanci. A gun taron manema labaru, Mr. Bush ya nuna cewa, idan Pakistan ta zama wata kasa da 'yan ta'adda su kan kai hare-hare, to, da kyar a sami nasarar yakin Afghanistan. Ya kuma kara da cewa, inganta hadin gwiwa a tsakanin Pakistan da Afghanistan a fannin yaki da ta'addanci zai ba da taimako sosai wajen yaki da 'yan tawayen da ke yankin kan iyakar kasashen 2. Ban da wannan kuma, ya yi bayanin cewa, Amurka ta bukaci ci gaba da hada kanta da Pakistan domin fafatawa da 'yan tawayen da ke yankin kan iyakar Pakistan da Afghanistan.

Dadin dadawa kuma, kafin wa'adin aikinsa ya cika, Mr. Bush yana son ya karfafa gwiwar sojojin Amurka da aka jibge a Afghanistan. Amurka ta yi shekaru 7 tana dukufa kan yakin Afghanistan, inda ko da yake ta yi ta tura karin sojojinta zuwa Afghanistan, amma dakarun Taliban sun kara samun karfi a maimakon su raunana. Robert Gates, ministan tsaron Amurka da ya kai ziyara a Afghanistan kafin Mr. Bush ya taba sanar da tura karin sojojin Amurka zuwa Afghanistan kafin lokacin zafi na shekara mai zuwa. A lokacin ziyararsa, Mr. Bush ya kuma nanata tura karin sojoji zuwa wannan kasa. Babu tantama wadannan bayanan da manyan jami'an Amurka suka yi sun karfafa gwiwar sojojin Amurka a Afghanistan.

An labarta cewa, a kwanan baya, gwamnatin Bush ta dudduba manyan tsare-tsare kan yakin Afghanistan, ta kuma fara tsara wani shiri domin tabbatar da samun nasarar yakin Afghanistan da kuma fitar da Amurka daga wannan yaki na tsawon shekaru da dama, wanda ya caza kan Amurka sosai. Amma duk da haka, saboda wa'adin aikin Mr. Bush zai cika ba da jimawa ba, watalika zai bar wannan shiri ga sabuwar gwamnati, sa'an nan kuma, zai bar wannan yaki na tsawon shekaru 7 da ba a ga karshensa ba tukuna ga wanda zai gaje shi.(Tasallah)


1 2