Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-16 15:52:04    
Bush ya ziyarci Afghanistan ba zato ba tsammani

cri

Bayan da ya kammala ziyararsa a kasar Iraq, a ran 15 ga wata, shugaba Bush na kasar Amurka ya isa birnin Kabul, hedkwatar kasar Afghanistan domin kai ziyara. Wannan shi ne karo na 2 da Mr. Bush ya kai wa Afghanistan ziyara bayan da ya zama shugaban Amurka, haka kuma ziyararsa ziyara ce ta yin ban kwana da ya kai wa Afghanistan kafin wa'adin aikinsa ya cika.

Mr. Bush ya kai wannan ziyara ne ba zato ba tsammani, ya yi wasu sa'o'i kawai yana ziyara a Afghanistan. Manazarta sun nuna cewa, ko da yake tsawon lokacin ziyarar Mr. Bush ya yi kadan, amma an danka masa babban nauyi a fannoni da dama.

Da farko, Mr. Bush ya yi amfani da ziyararsa domin jaddada sakamakon da aka samu daga wajen yakin Afghanistan da ya ta da. A filin jirgin sama na Bagram, Mr. Bush ya bayyana cewa, Afghanistan ta sha bamban bisa yadda ta taba kasancewa yau da shekaru 7 da suka wuce, ta sami kyautatuwa sosai a fannoni da yawa. Amma ya kuma amince da cewa, ya zuwa yanzu yawan tashe-tashen hankula da ake samu a wannan kasa na karuwa. Duk da haka, Mr. Bush yana ganin cewa, dalilin da ya sa haka shi ne Amurka ta girka sojojinta zuwa wuraren da ba a taba girke sojoji a da ba, ta haka dakaru sun mayar da martani mai tsanani.

Sa'an nan kuma, Mr. Bush ya isar da sako ga gwamnatin Afghanistan na samun goyon baya daga sabuwar gwamnatin Amurka a gabannin lokaci. A lokacin ziyararsa, Mr. Bush ya bayyana wa gwamnatin Afghanistan cewa, babu abin da zai hana gwamnatin Afghanistan ta ci gaba da samun goyon baya daga Amurka, yayin da sabon shugaba zai kar?i ragamar mulki a fadar White House. Yau da shekaru 7 da suka wuce, Mr. Bush ya ta da yakin Afghanistan, inda aka hambarar da gwamnatin Taliban, amma a shekarun nan, dakarun Taliban suna son sake dawowa. Ya rage sauran kwanaki 30 ko fiye ga Mr. Bush kafin ya cika wa'adin aikinsa. A kwanan baya, Barac Obama, mai jiran gadon shugabancin Amurka ya bayyana cewa, zai mayar da Afghanistan a matsayin muhimmin fagen yaki da ta'addanci, a maimakon Iraq. A gun taron manema labaru da Mr. Bush da takwaransa na Afghanistan Hamid Karzai suka yi cikin hadin gwiwa, Mr. Bush ya ce, Afghanistan za ta iya dogara da sabuwar gwamnatin Amurka, kamar yadda take dogara da gwamnatin Amurka ta yanzu.


1 2