Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-15 16:53:44    
An kara saurin gina tashar ruwa ta Shanhaiguan a birnin Qinhuangdao na kasar Sin

cri

Kamfanin sarrafa abinci na Jinhai da ke birnin Qinhuangdao wani babban kamfani ne mai jarin waje da ke sarrafa amfanin gona, kuma ke samar da man girki da sauran kayayyaki na waken soya. Yana kuma samar da kayayyakinsa a kasuwar cikin gida ta kasar Sin da sauran kasuwannin kasashen da ke makwabtaka da kasar Sin. Mr. Li Yankang wanda ke kula da aikin sufurin kayayyakin wannan kamfani ya gaya wa wakilinmu cewa, an kafa masana'antun sarrafa waken soya ne a wurin da ke kusa da tashar ruwa ta Shanhaiguan domin neman samun sauki wajen samun danyun kayayyakin da yake bukata da sufurin gyararrun kayayyakin da ya sarrafa. Sakamakon haka, kamfani ya yi tsimin kudaden yin kayayyaki da ya kashe. Mr. Li ya ce, "Yawan danyun kayayyakin da muke bukata a kowace shekara ya kai kimanin ton dubu dari 5, kuma muna samar da gyararrun kayayyaki ton dubu dari 3. Idan mun yi amfani da motoci wajen sufurin kayayyakinmu, za mu kashe kudade masu yawan gaske. Muna samun galibin danyun kayayyaki ne daga yankunan arewa maso gabashin kasarmu, yanzu muna sufurinsu daga yankunan arewa maso gabashin kasar ta hanyar dogo zuwa Shanhaiguan, sannan mu yi sufurin gyararrun kayayyakin da muka sarrafa zuwa kasashen Japan da Koriya ta kudu ta jiragen ruwa daga tashar ruwa ta Shanhaiguan."

Ya zuwa yanzu, kamfanonin sarrafa amfanin gona na kasashen duniya da na kasar Sin sun riga sun kafa masana'antunsu a unguwar raya tattalin arizki da fasahohin zamani ta Qinhuangdao. Ya zuwa karshen farkon rabin shekarar da muke ciki, jimlar kudaden da wadannan masana'antun sarrafa amfanin gona suka samu ta riga ta kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 2. Sabo da haka, wannan unguwa ta riga ta zama sansanin sarrafa amfanin gona da man girki mafi girma a arewacin kasar Sin.

Amma, unguwar raya tattalin arziki da fasahohin zamani ta Qinhuangdao tana da babban burin da take kokarin cimmawa, wato ana fatan wannan unguwa za ta iya taka karin rawa wajen raya tattalin arzikin birnin Qinhuangdao da na sauran wuraren da ke makwabtaka da ita, har ma na yankunan arewa maso gabashin kasar Sin. Mr. Hu Yingjie ya ce, "Tashar ruwa ta Shanhaiguan tana wurin da ke hada yankunan arewacin kasar Sin da yankunan arewa maso gabashin kasar. Bisa shirin da muka tsara, ya kamata tashar ruwa ta Shanhaiguan ta zama wani wurin da ke jigilar kayayyaki na yankunan arewa da yankunan arewa maso gabashin kasar Sin. Bayan an kaddamar da tashar ruwa ta Shanhaiguan, tabbas ne za ta iya bayar da gudummowarta kamar yadda ya kamata wajen raya tattalin arzikin yankunan da ke makwabtaka da ita." (Sanusi Chen)


1 2 3