Birnin Qinhuangdao wanda ke fiye da kilomita 280 da ke gabas da birnin Beijing na daya daga cikin muhimman biranen da ke da tasoshin ruwa a arewacin kasar Sin. A shekarar 1984, an soma kafa unguwar raya tattalin arziki da fasahohin zamani ta birnin Qinhuangdao, wato na daya daga cikin unguwannin raya tattalin arziki 14 wadanda suke matsayin kasa, kuma aka kafa su a gabanin sauran unguwannin raya tattalin arziki na kasar. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, birnin Qinhuangdao yana kokarin gina wata sabuwar tashar ruwa, wato tashar ruwa ta Shanhaiguan domin kokarin kyautata tsarin masana'antunsa.
Akwai wata tashar ruwa wadda ba ta samu kankara a lokacin sanyi ba kuma aka gina ta yau fiye da shekaru dari 1 da suka gabata a birnin Qinhuangdao. Yawan kayayyakin da ake jibge su a tashar ya kai fiye da ton miliyan dari 2 a kowace shekara. Sabo da haka, wannan tashar ruwa ta Qinhuangdao tana daya daga cikin manyan tasoshin ruwa na duniya. Amma a cikin 'yan shekarun da suka gabata, wannan tashar ruwa ba ta iya biyan bukatun da ake da su ba a birnin Qinhuangdao sakamakon cigaban tattalin arzikinsa cikin sauri. Sakamakon haka, an tsai da kudurin gina wata sabuwar tashar ruwa a Shanhaiguan, inda za a iya hada yankunan arewacin kasar Sin da yankunan arewa maso gabashin kasar. Mr. Hu Yingjie, shugaban kwamitin sa ido da tafiyar da unguwar raya tattalin arziki da fasahohin zamani ta birnin Qinhuangdao ya bayyana cewa, "Yanzu ana gina wannan tashar ruwa. Wasu masana'antu sun riga sun shiga unguwarmu sabo da muna da wannan tashar ruwa. Sabo da haka, wasu masana'antu wadanda suke kera manyan injuna ko suke sarrafa kayayyaki iri iri suka zo unguwarmu don soma yin shawarwari tare da mu. A da, ba zai yiyuwa ba ne irin wadannan masana'antu su zuba jari a wurin da unguwarmu ke ciki. Tashar ruwa da ake ginawa tana sa kaimi ga cigaban masana'antun da suke bukatar wannan tashar ruwa."
Kamfanin sufurin injunan samar da wutar lantarki na Harbin yana sufurin injuna da na'urorin da kamfanonin samar da wutar lantarki suke bukata. Yana matsayin gaba a cikin takwarorinsa a nan kasar Sin. A shekara ta 2003, wannan kamfani ya soma kafa ofishinsa a unguwar raya tattalin arziki da fasahohin zamani ta Qinhuangdao. Ya kuma zuba jari kan tashar ruwa da ake ginawa a Shanhaiguan. Sakamakon haka, ya samu ikon yin amfani da wannan tashar ruwa na shekaru 10. Mr. Yu Shaotong, mataimakin babban direktan wannan kamfani ya ce, "Kamfaninmu yana bukatar tashar ruwa da ke da sharadin musamman, wato dole ne injin din daga kaya zai iya daga kaya mai nauyi sosai. A yawancin tasoshin ruwa, ana da injunan daga kaya da suke iya daga kaya na nauyin kimanin ton 20 ne kawai, amma galibin injunan da muke sufuri suna da nauyi fiye da ton 30 ko 40 ko fiye. Sabo da haka, galibin tasoshin ruwa na kasuwanci ba su iya biyan bukatunmu. Amma a wannan tashar ruwa ta Shanhaiguan, ana da irin wannan injin da zai iya daga kaya mai nauyi da muke bukata."
1 2 3
|