Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-11 17:45:20    
Hukumar UNHCR na kokarin neman mafita ga dimbin 'yan gudun-hijira

cri

Matsalar 'yan gudun-hijira, matsala ce da ta dade tana ciwa kasashen duniya tuwo a kwarya. A wajen taron da aka shirya a wannan rana, firaministan kasar Tanzaniya Mizengo Kayanza Peter Pinda ya gabatar da bayanin yadda kasarsa ke shirin warware wannan matsala, inda ya ce, kamata ya yi gamayyar kasa da kasa su sa kulawa sosai kan gungun mutane masu gudun-hijira, haka kuma kada su manta da irin kokarin da kasashe masu karbar 'yan gudun-hijira suke yi. A hakika dai, bisa kididdigar da hukumar UNHCR ta bayar, an ce, a halin yanzu, kasashe masu tasowa suna kokarin karbar akasarin 'yan gudun-hijira a duniya. Babban kwamishina mai kula da harkokin 'yan gudun-hijira na MDD, Antonio Guterres ya ce, daidaita matsalar 'yan gudun-hijira yadda ya kamata, nauyi ne dake rataye a wuyan dukkanin kasashen duniya. Ya kamata kasashen duniya su kafa wani tsari na daukar nauyi cikin adalci, a wani yunkurin daukar matakai na bai daya domin warware wannan matsala.

Kazalika kuma, hukumar UNHCR ta sake jaddada cewa, tallafawa 'yan gudun-hijira, babban nauyi ne da aka dankawa kowace kasa. UNHCR ta kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su kara bada tallafin kudi wajen kyautata halin matsugunan 'yan gudun-hijira da samar da agajin jin-kai, domin warware matsalar 'yan gudun-hijira daga dukkan fannoni, da neman mafita ga 'yan gudun-hijira masu tarin yawa.(Murtala)


1 2