Hukumar kula da harkokin 'yan gudun-hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR ta shirya shawarwarin yini biyu ranar 10 ga wata a fadar Palais Des Nations a birnin Geneva na kasar Switzerland, hedkwatar MDD dake nahiyar Turai, inda aka tattauna kan yadda za'a yi domin neman mafita ga mutane kimanin miliyan 6 da suke gudun-hijira a wurare daban-daban na duniya, da yin kira ga kasashen duniya da su maida hankulansu kan wannan lamari da nuna goyon-bayansu.
Shawarwarin sun samu halartar jami'an gwamnatocin kasashe sama da 50, da wakilai fiye da 300 daga hukumomin kasa da kasa da kungiyoyin da ba na gwamnati ba, inda suka mayar da hankali kan harkokin masu gudun-hijira kimanin miliyan 6 wadanda suka shafe tsawon shekaru 5 ko fiye suna gudun-hijira. Hukumar UNHCR ta ce, an shirya shawarwarin tare da zummar jawo hankalin daukacin duniya, a wani kokarin gano bakin zaren daidaita matsalar 'yan gudun-hijira.
Wani rahoto daga hukumar UNHCR ya ce, tun daga farkon shekarun 1990, an samu tashe-tashen hankula da fadace-fadacen da suka ki ci suka ki cinyewa a yankin Balkan, da yankin babban tafki na Afirka, gami da kasashen Sudan da Chadi da Iraki, inda dimbin mutane suka bar matsugunansu suka fara gudun-hijira. Akasarin masu gudun-hijira sun tsere zuwa kasashe makwabta, inda suke yin dafifi a yankunan bakin iyaka da sansanonin 'yan gudun-hijira dake yankunan karkara. Ba ma kawai masu gudun-hijira sun haddasa cikas ga muhallin halittu, da albarkatun kasa, da sha'anin samar da guraben aikin yi na wuraren da suke jibgeba, hatta ma suna zama cikin halin tsaka mai wuya. Baligai sun kasa samun guraben aikin yi, yara kanana ba su da damar shiga makaranta, har ila yau kuma an gaza wajen biyan bukatun masu gudun-hijira na yau da kullum. A waje daya kuma, halin kaka-naka-yi da ake ciki a sansanonin masu gudun-hijira ya haddasa matsaloli da dama, ciki har da barkewar cututtuka masu yaduwa, da munanan laifuffukan fasa-kwaurin makamai, da sace yara kanana.
1 2
|