Ghana ta riga ta zama wurin da ake kirar tarurukan kasa da kasa masu muhimmanci. Tarurukan da aka yi a kasar Ghana a shekarar bana, sun hada da bikin baje koli na cinikayya da raya kasa na MDD, da bikin MDD kan sauyin yanayi, da bikin kasashen Afirka da na tekun Caribbean, da dai makamantansu. Wannan ya sa kasar Ghana ta kara kwarjininta a cikin kasashen duniya, haka kuma ya sa mutanen kasar suka kara yin alfahari. Jama'ar kasar Ghana sun mai da kasarsu abar koyi ga kasahen Afirka, shi ya sa ba za su yarda da an bata sunanta sakamakon takaddamar zabe ba.
Kwamitin zabe na kasar Ghana shi ma ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali cikin zaben da aka yi. Kwamitin na da 'yancin kasnsa, ya iya aiwatar da aikinsa ba tare da samun matsin lamba daga jam'iyyun siyasa ba, ta hakan an magance magudin da ka iya samu cikin zabe. Tun da kasar ta fara yin zabe a shekarar 1992, kwamitin zaben kasar ya yi wa tsarin zabe kwaskwarima, hatta ma an gyara takardun kuri'a da akwatunan kuri'a, ta yadda an iya yin zabe a bayyane don jama'a su gani.
A baya ga haka kuma, wayin kan jama'ar Ghana kan zabe daya ne daga cikin dalilan da suka sa aka samun kwaciyar hankali a zaben kasar Ghana. A lokacin zabe, kungiyoyin jama'ar kasar, tare da kafofin watsa labaru, suna kokarin wayar da kan jama'a, dangane da ra'ayin da ya kamata a nuna wa zaben.(Bello Wang) 1 2
|