Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-08 16:38:47    
Don me an gudanar da zabe cikin lumana a kasar Ghana

cri

Cikin shirin yau, za mu yi muku bayani kan kada kuri'a don zaben shugaban kasa da wakilan majalisar dokoki da aka aiwatar da shi a kasar Ghana, wanda aka ce an fara yinsa ne a ran 7 ga watan Disamba da karfe 7, haka kuma an kawo karshensa ne da karfe 5 da yamma. An kada kuri'ar cikin kwaniyar hankali, ba tare da wata takaddama ba. Da ma, kafin an fara jefa kuri'a a kasar Ghana, an nuna damuwa kan zaben, bisa ganin zaune tsaye da tarzomar da aka samu a kasashen Zimbabwe da Kenya da dai sauran kasashen Afirka, lokacin da aka yi babban zabe. Manazarta na ganin cewa, dalilin da ya sa aka iya kada kuri'a a kasar Ghana cikin kwanciyar hankali, shi ne domin cigaban tattalin arziki da hadin kan al'ummomi da aka samu a kasar a shekarun baya.

Bayan da shugaba Kufuor na kasar Ghana ya kama ragamar mulki, tattalin arzikin kasar yana bunkasuwa cikin sauri, har ma ya ci gaba da karuwa da kashi 6% cikin shekaru 2 da suka wuce. Matakan da shugaba Kufuor ya dauka na kara zuba jari don gina ayyukan more rayuwar jama'a da inganta ayyukan ilimi da kiwon lafiya, sun sa zaman rayuwar jama'a ya kyautu, kuma al'umma na cikin halin kwaciyar hankali. Ban da hakan kuma, kabilun kasar Ghana na zaman tare cikin lumana, suna auratayya tsakanin juna. Haka kuma, shugabannin kasar na da sun zo daga kabilu daban daban, shi ya sa jam'iyyun siyasar kasar ba su iya ta da kin jinin juna a tsakanin kabilun ba.

Cikin shekaru 3 da suka wuce, kasar Ghana ta gamu da abubuwan alheri daya bayan daya. Kungiyar kasar ta shiga cikin kungiyoyi 8 mafi kwarewa a karon farko cikin gasar kwallon kafa ta neman cin kofin duniya ta shekarar 2006. A shekarar 2007, an yi bikin zagayowar rana ta cika shekaru 50 da aka samu 'yancin kan kasar Ghana. Haka kuma, a shekarar 2008, kasar ta samu nasarar shirya gasar kwallon kafa ta neman cin kofin kasashen afirka. E. Gyimah-Boadi, darektan cibiyar raya dimokuradiyya ta kasar Ghana, ya ce, abubuwan 3 da muka ambata sun karfafa hadin gwiwar jama'ar kasar, shi ya sa, bisa halin da ake ciki, ba zai yiwu an samu tashin hankali a kasar a sabili da zabe ba. A ganinsa, jama'ar kasar suna samun jin dadin zama, har wa yau kuma, 'yan takarar shugabancin kasar dukkansu sun dau alkawarin bunkasa tattalin arzikin kasar.

1 2