Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-04 16:27:06    
Zumuncin dake tsakanin kasar Sin da Pakistan zai dade

cri

Shahbaz Nadir,dalibi ne na aji na uku mai koyon ilimin kudade a jami'ar koyon kasuwanci ta Karachi.ya taba kai ziyara a kasar Sin daga karshen watan Yuli zuwa farkon watan Augusta na bana a matsayin kungiyar matasa dari ta Pakistan. Yayin da ya ke takalo abin da ya ji ko ya gani a kasar Sin farin cikin ya rufe shi,ya ce

"Kasar Sin ta ba ni alamu masu kyau sosai,mutanen Sin suna so su taimaki saura tare da aminci.motocin gari sun zirga zirga yada ya kamata,mutane na tafiya a hanyoyin da aka kebe musu,matukan motocin su kan tsaya a wurin da aka kebe domin matafiya.kasar Sin babbar aminiya ce ta kasar Pakistan,babban albishiri gare da kasar Sin ta cimma nasarar shirya wasannin Olympics a Beijing."

Jiang Xueying,wani dan kungiyar matasa ta Sin shi akawun gwamnatin ne a halin yanzu da ya kammala kartunsa ajami'a a yanayin zafi na bana, ba shi da masaniya game da Pakistan kafin wannan ziyara. Bayan da ya yi mu'amala da mutanen Pakistan musamman matasan cikin 'yan kwanaki a ziyarrsa, surar Pakistan ta bayyanu a zuciyarsa. Ya ce

"A hakika Pakistan ta ba ni alamu masu kyau.Mutanen Pakistan suna da zafin nama da hazaka.A dukkan hanyoyin da muke bi wajen ziyara da akwai mutane Pakistan da suka yi mana jinjina da gaisuwa."

Jiang Xueying ya gaya wa wakilinmu cewa ya sami wata aminiyar Pakistan a birnin Beijing,wannan amininiyarsa ta ba shi taimako babba a wannan gami yayin da yake ziyara a kasar Pakistan.

"Lokacin da na ke kallon wasanin Olympics a birnin Beijing,na sami wata dalibar kasar Pakistan da take karatu a kasar Sin.kamar sauran mutanen Pakistan suke ita ma tana da zafin nama, ta gaya mini wuraren sayar da hajoji da nuna mini hanyoyin zuwa wuraren da kuma fadakar da ni kan abubuwan da ya kamata in sa lura a kai a kasar Pakistan ta yi mini bayani fila fila."

Da ziyarar kungiyar matasa ta kasar Sin ta kusan kaiwa karshe,firayim minista na kasar Pakistan Yousaf Raza Gilani ya gana da kungiyar matasa ta kasar Sin a fadarsa a birnin Isalambad,babban birnin kasar Pakistan.A lokacin ganawar,Girani ya yaba da dangantakar dake tsakanin Sin da Pakistan.Ya ce

"Dangantaka dake tsakaninmu da kasar Sin wani muhimmin kashi ne a cikin manufarmu ta harkokin waje, mun yi farin ciki da alfahari da kasancewar zumuncin a tsakanin Pakistan da Sin. Dangantaka dake tsakanin mu ta kasance yadda ya kamata a koyaushe,zumuncin dake tsakanin kasashenmu biyu bai canza ba kome ya faru a bangarori da duniya ko sauyin yanayin siyasa da canjn shugabani a kowace kasa tasu. Firayim minista Gilani ya kuma sa fatan alheri ga mu'amalar da matasan Sin da na Pakistan suke yi tsakaninsu da ci gaban amincin dake tsakaninsu.


1 2 3