Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-01 17:34:45    
Ana gano cigaban da kasar Sin ta samu a fannin cinikin waje sakamakon sauyin "Bikin cinikin waje na Guangzhou"

cri

Shehun malami Mei Xinyu ya nazarci cewa, cigaban da aka samu a gun bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice na Guangzhou yana kuma bayyana yadda ake canja tsarin kayayyakin da ake shige da fice a nan kasar Sin. An samu wannan sauye-sauye ne sabo da kasar Sin tana kokarin kyautata tsarin tattalin arziki da canja hanyar raya tattalin arzikinta. Mr. Mei ya ce, "A da, kasar Sin ta fitar da danyen kayayyaki zuwa kasashen waje tare da shigar da gyararrun kayayyakin da aka sarrafa, amma yanzu yawan gyararrun kayayyakin da aka sarrafa, musamman injuna da na'urorin lantarki da kasar Sin ke fitarwa suna ta samun karuwa, a waje daya, yawan danyen kayayyakin da take shigowa daga kasashen waje yana kuma karuwa. Wato tsarin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice ya kasance kamar wata kasa mai masana'antu ke shige da fice."

Bugu da kari kuma, wadanda suke halartar bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice na Guangzhou suna kuma canzawa. A shekarar 1999, kamfanoni masu zaman kansu wadanda suka samun izinin shige da ficen kayayyaki da kansu sun soma halartar bikin. Ya zuwa bikin na karo 103 da aka yi a lokacin bazara na shekara ta 2008, yawan kudaden cinikin waje da kamfanoni da masana'antu masu zaman kansu suka samu ya kai fiye da dala biliyan 22, wato ya kai kashi fiye da rabi bisa na dukkan kudaden cinikin waje da aka samu a gun wancan biki. A cikin shekarun da ba su kai 10 ba, kamfanoni masu zaman kansu sun riga sun zama muhimmin jigo a gun bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice na Guangzhou.

Kafin shekara ta 2007, sunan wannan biki shi ne "bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa na Guangzhou", amma a shekara ta 2007, an canja wannan suna da ya zama "bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice na Guangzhou". Mr. Song Hong wanda ke aiki a cibiyar nazarin kimiyyar zaman al'umma ta kasar Sin ya ce, lokacin da kasar Sin ta soma yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje yau da shekaru 30 da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta sa kaimi ga kamfanoni da masana'antu da su fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje domin neman kudaden musanya da kyautata karfinsu na kawo albarka a gida. Amma a cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, kasar Sin ta samu rarar kudaden musanye masu dimbin yawa. Lokacin da wadannan dimbin rarar kudaden musanye ke kawo wa kasar Sin wadata, sun kuma zama muhimmin dalilin da ya sa aka ta da kiki-kaka a fannin cinikin waje a tsakanin kasar da kasashen waje. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta soma aiwatar da manufofin neman daidaito a fannin cinikin waje. Mr. Song ya ce, "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, mun dauki muhimman matakai bisa manyan tsare tsare domin kokarin samun daidaito a fannin cinikin waje, wato lokacin da take tabbatar da karuwar kayayyakin da take fitarwa, tana kokarin kara kayayyakin da take shigo da su daga kasashen waje."

Tun daga bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice na Guangzhou na karo na 101, an kafa wata unguwar nune-nunen kayayyakin da ake shigar da su daga kasashen waje. Madam Jan Wilson wadda ta zo daga jihar Washington ta kasar Amurka ta bayyana cewa, "Wannan ne wani babban bikin cinikin kayayyaki na duniya, kuma ana ta kara fadinsa. A gun bikin, za mu iya samun bakin da suka zo daga duk duniya. Muna fatan mu samu baki a gun bikin, kuma mu samu wasu 'yan kasuwa da za su iya sayar da kayayyakinmu a nan kasar Sin."

A cikin shekaru da yawa da suka gabata, an samu sauye-sauye sosai a gun bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice na Guangzhou. Alal misali, yawan sanannun kamfanoni na kasa da kasa da suke halartar wannan biki yana ta karuwa. Mr. Song Hong yana ganin cewa, wannan ya almanta cewa, kayayyaki kirar kasar Sin suna kara karfinsu na yin takara a kasuwannin duniya, kuma karfin samar da kayayyaki kirar kasar Sin a kasuwannin duniya ya samu ingantatuwa. Mr. Song ya ce, "Sabo da karfin samar da kayayyaki da na yin cinikin waje na kasar Sin sun samu ingantatuwa. Ba ma kawai baki 'yan kasuwa sun sayi wasu kayayyakin da Sinawa wurin suka yi ba, har ma manyan kamfanoni na kasa da kasa, kamar kamfanin Wal-Mart suna kuma soma sayen kayayyaki kirar kasar Sin a gun bikin. Wannan ya almanta cewa, aikin bude kofar kasar Sin ya samu cigaba sosai, kasar Sin tana hada kanta da sauran kasashen duniya a fannin tattalin arziki." (Sanusi Chen)


1 2