Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-01 17:34:45    
Ana gano cigaban da kasar Sin ta samu a fannin cinikin waje sakamakon sauyin "Bikin cinikin waje na Guangzhou"

cri

"Bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice na Guangzhou" da aka yi a birnin Guangzhou na lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin biki ne da aka yi a karo na 104. An shirya bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice na Guangzhou da aka saba shiryawa sau biyu a kowace shekara tun daga shekarar 1957, wato an shirya wani a lokacin bazara, sannan an shirya wani daban a lokacin kaka. Sabo da haka, ya riga ya zama bikin cinikin waje da ya fi dadewa kuma ya fi girma a kasar Sin. Sakamakon haka, a kan siffanta wannan biki cewa, tana almanta halin da ake ciki a kasar Sin a fannin cinikin waje. Kuma a kan samu dimbin bayanai game da halin da kasar Sin ke ciki a fannin cinikin waje da manufofin cinikin waje da kasar Sin ke aiwatarwa.

Mr. Wen Yangsong, babban direkta ne na wani kamfanin cinikin waje na lardin Guangdong. Wannan ne karo na 86 da ya halarci bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice na Guangzhou da aka yi a lokacin kaka na shekarar da muke ciki. Yau da shekaru 43 da suka gabata, Mr. Wen, wato wani saurayi ya halarci bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice na Guangzhou a matsayin mai sayen kayayyaki na kamfaninsa na yanzu. Lokacin da yake tunawa da halin da ake ciki a wancan lokaci, Mr. Wen ya ce, "A wancan lokaci, tufafin da muka sanya tufafi ne masu launin shude ko masu launin toka-toka. Amma tufafin da baki 'yan kasuwa suka sanya suna da salo da launuka iri iri. Ba mu iya sabawa da tufafin da suka sanya ba. Bugu da kari kuma, a wancan lokaci, ana karancin wadanda suka iya harsunan waje. Baki 'yan kasuwa sun yi mamaki sosai sabo da na iya yin hira da su da harshen Turanci."

A shekarar 1957 ce aka soma bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa na Guangzhou na lardin Guangdong. A wancan lokaci, bai cika shekaru 10 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ba, kasashen yammacin duniya sun sanya takunkumi kan kasar Sin a fannin tattalin arziki. Mr. Mei Xinyu, kwararre wanda ke nazarin cinikin waje ya bayyana cewa, bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa na Guangzhou yana da ma'anar musamman, kuma an dora nauyin musamman a kansa a cikin wannan halin da ake ciki. Mr. Mei ya ce, "Bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa na Guangzhou bikin cinikin waje ne da kasar Sin ta kafa domin cimma burinta na shigar da ita zuwa kasuwannin kasashen waje da kuma raya cinikin waje a nan kasar Sin."

A hakika dai, an bude kofar yin cinikin waje a tsakanin kasar Sin da kasashen waje bayan da aka soma wannan bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa na Guangzhou. Lokacin da aka soma shirya bikin na farko a shekarar 1957, yawan baki 'yan kasuwa da suka halarci wannan biki ya kai 1200 kawai. Yawan kudaden cinikin waje da aka samu ya kai dalar Amurka miliyan 17 kawai. Amma ya zuwa shekara ta 2008, lokacin da ake yin bikin cinikin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice na Guangzhou na lokacin bazara a karo na 103, yawan 'yan kasuwa da suka halarci wannan biki ya kai fiye da dubu 190, yawan kudaden cinikin waje da aka samu a gun wannan biki ya kai dalar Amurka biliyan 38.2. Bugu da kari kuma, jimlar kudaden cinikin waje da kasar Sin ta samu a shekarar 1957 ta kai dalar Amurka biliyan 3.1 kawai, amma ya zuwa karshen shekara ta 2007, wannan adadi ya zama biliyan 2000.

Mr. Wen Yangsong wanda ya taba halartar bukukuwan cinikin kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice na Guangzhou har sau da yawa ya ce, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, ire-iren da ake ciniki a gun bikin sun samu canzawa sosai. A da, an fitar da kayayyakin da mutanen wurin ke yi da danyen kayayyaki kawai daga kasar Sin, amma yanzu ana fitar da kayayyaki iri iri a gun wannan biki. Mr. Wen ya ce, "Yanzu ana kuma fitar da na'urorin samarin samaniya da kayayyakin man fetur da kayayyakin man gas da kuma kayayyaki masu fasaha."


1 2