Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-27 17:44:49    
Ziyarar da Hu Jintao ya yi a kasashen Latin Amurka da Giriki ta samu nasara sosai

cri

A waje daya kuma, a gun taron kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, Hu Jintao ya kuma bayar da ra'ayoyi biyar game da batutuwan da suke jawo hankalin bangarori daban daban a duk duniya baki daya. Mr. Hu ya ce, ya kamata a samu ra'ayi bai daya wajen ciyar da tsarin yin cinikayya a tsakanin bangarori daban daban gaba kamar yadda ya kamata. Sannan kuma ya kamata a sauke nauyin da ke bisa wuyansa wajen tinkarar sauyin yanayin duniya. Haka kuma, ya kamata a kara yin mu'amala da hadin guiwa domin fama da bala'u daga indallahi tare. Bugu da kari kuma, ya kamata a tabbatar da nauyin zaman al'umma da ke bisa wuyan masana'antu. Daga karshe dai, ya kamata a daidaita ayyukan da ake yi domin tabbatar da samar da isashen hatsi da makamashin da ake bukata.

Haka kuma, Yang Jiechi ya ce, ziyarar da Hu Jintao ya yi ta karfafa dangantakar sada zumunta irin ta hadin guiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka da kuma a tsakanin kasar Sin da kasar Giriki. Lokacin da yake ziyara a kasar Peru, a gun majalisar kafa dokoki ta kasar Peru, Mr. Hu ya bayar da wani jawabi mai lakabi "Kafa dangantakar abokantaka irin ta hadin guiwa daga dukkan fannoni a tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka a cikin sabon lokaci". A cikin wannan jawabinsa, ya bayyana wa duk nahiyar Latin Amurka matsayi da matakan da kasar Sin ke dauka wajen raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Latin Amurka baki daya. Mr. Hu ya ce, ya kamata a ci gaba da karfafa dangantakar siyasa da ke kasancewa a tsakaninsu, kuma a karfafa hadin guiwa irin ta moriyar juna a fannonin tattalin arziki da cinikayya, sannan a kara yin hadin guiwa da daidaitawa kan harkokin kasa da kasa. Haka kuma ya kamata a kara mai da hankali kan yin koyi da juna da neman cigaba tare a fannin zaman al'umma da kuma kara yin mu'amala kan abubuwan da ke shafar rayuwar dan Adam na yau da kullum a tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka. (Sanusi Chen)


1 2