Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-27 17:44:49    
Ziyarar da Hu Jintao ya yi a kasashen Latin Amurka da Giriki ta samu nasara sosai

cri

A ran 26 ga wata, bayan da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kammala ziyararsa a kasashen Latin Amurka da Giriki, a kan hanyar dawowarsa a kasar Sin, Mr. Yang Jiechi, ministan harkokin waje na kasar Sin wanda ya raka shugaba Hu Jintao ya bayyana wa manema labaru sakamakon da aka samu a cikin wannan ziyara. Mr. Yang ya ce, ziyarar da shugaba Hu Jintao ya yi ta cimma burin karfafa zumunta da kara amincewa da juna da kara yin hadin guiwa da kuma neman cigaba tare a tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka da Giriki.

Bayan da ya halarci taron shugabannin rukunin kasashe 20 kan batun hada hadar kudi ta duniya da taron koli kan batun tattalin arzikin duniya da aka yi a birnin Washington na kasar Amurka, tun daga ran 17 zuwa ran 26 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya halarci kwarya kwaryar taron shugabannin kasashen Asiya da na tekun Pacific, wato APEC da aka yi a karo na 16 a birnin Lima na kasar Peru, kuma ya kai ziyara ga kasashen Costa Rica da Cuba da Peru da Giriki.

Mr. Yang ya bayyana cewa, shugaba Hu Jintao ya yi wannan ziyara ne lokacin da ake tinkarar matsalar hada hadar kudi mai tsanani a duniya, kuma dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka da kasar Giriki tana cikin sabon lokaci. Tabbas ne wannan ziyara tana da muhimmiyar ma'ana wajen kara yin hadin guiwa a tsakanin kasa da kasa domin tinkarar matsalar hada hadar kudi tare da kuma ciyar da dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka da kasar Giriki gaba.

Mr. Yang Jiechi ya ce, lokacin da yake halartar taron shugabannin kungiyar APEC, Hu Jintao ya bayyana matsayin da bangaren Sin ke dauka kan batun tinkarar matsalar hada hadar kudi da batun yadda za a yi kwaskwarima kan tsarin hada hadar kudi na duniya. Shugabanni mahalartar taron sun yaba kuma sun mai da martani kan jawabinsa. Ra'ayoyin jama'a na duniya sun kuma yaba wa gwamnatin kasar Sin sabo da ta dauki jerin matakan habaka bukatu a kasuwannin gida da raya tattalin arzikinta da kuma tinkarar hada hadar kudi da ta auku a duk duniya.

1 2